Skip to content
TimesPosts homeTimesPostsThe record, as it happens.

An kama mutane 5 da ake zargi da lalata fastocin Tinubu da Abba yayin raka Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero

An kama mutane 5 da ake zargi da lalata fastocin Tinubu da Abba yayin raka Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero Rundunar ƴansandan Jihar Kano ta kama mutum biyar da ake zargi da lalata allunan…

Ay Abdullahi · Admin

· 1 min read

An kama mutane 5 da ake zargi da lalata fastocin Tinubu da Abba yayin raka Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero

Rundunar ƴansandan Jihar Kano ta kama mutum biyar da ake zargi da lalata allunan tallace-tallace da fastocin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Gwamna Abba Kabir Yusuf da wasu ’yan siyasa a jihar.

Kwamishinan ’yansandan jihar, Ibrahim Adamu Bakori, ne ya bayyana hakan yayin da yake amsa tambayoyin ’yan jarida kan matakan tsaro da kuma aiwatar da dokar hana hawan doki a bainar jama’a a Kano.

Bakori ya ce an kama mutanen ne bayan gudanar da bincike kan lalata kadarori da aka samu a lokacin da tsohon Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero ya yi hawa da kuma rikicin da ya biyo bayan batun hawan doki da jerin gwanon jama’a a jihar.

Ya ce an kammala binciken kuma an gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu, yana mai cewa rundunar za ta ci gaba da daukar matakin doka kan duk wanda aka samu da laifin da ka iya barazana ga zaman lafiyar jama’a.

Kwamishinan ya kara da cewa kamen ya biyo bayan wata fita da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ya yi a ranar Lahadi.

A cewarsa, rahotanni sun nuna cewa wasu daga cikin mutanen da suka raka Sarkin sun lalata fastoci da allunan tallace-tallace na Shugaba Tinubu, Gwamna Abba Kabir Yusuf da sauran ’yan siyasa.

Ya ce lamarin ya kara dagula yanayin zaman lafiya a jihar, musamman ganin yadda takaddamar masarautar Kano ke ci gaba da kasancewa.

More from TimesPosts