Ɗan majalisar wakilan Najeriya, Alhassan Ado-Doguwa, ya yi iƙirarin cewa albashin sabon ma’aikacin Hukumar Kula da Albarkatun Man Fetur ta Najeriya (NUPRC) ya ninka nasa sau 3
Ɗan majalisar wakilan Najeriya, Alhassan Ado-Doguwa, ya yi iƙirarin cewa albashin sabon ma’aikacin Hukumar Kula da Albarkatun Man Fetur ta Najeriya (NUPRC) ya ninka nasa sau 3.Doguwa, wanda ke…
Ay Abdullahi · Admin
· 1 min read

Ɗan majalisar wakilan Najeriya, Alhassan Ado-Doguwa, ya yi iƙirarin cewa albashin sabon ma’aikacin Hukumar Kula da Albarkatun Man Fetur ta Najeriya (NUPRC) ya ninka nasa sau 3.
Doguwa, wanda ke wakiltar mazaɓar Doguwa/Tudun Wada a Jihar Kano, ya ce albashinsa na wata a matsayin ɗan majalisa ya kai naira 616,000.
Ya kuma yi magana kan batun Political Exposure, yana mai cewa an nemi wasu ma’aikatan Babban Bankin Najeriya (CBN) su bayyana alaƙarsu da mutanen da ke da manyan muƙaman siyasa a lokacin da ake shirin rage yawan ma’aikata.
A cewarsa, an kuma bai wa wasu ma’aikatan damar barin aiki bisa wani tsari da zai ba su kuɗin da ya yi daidai da albashin shekaru 5 ko 10, ciki har da ɗansa.
Doguwa ya kuma yi iƙirarin cewa idan wani ɗan majalisa ya rasu, ana cire naira 100,000 daga asusun kowane ɗan majalisa domin taimaka wa iyalan mamacin.
More from TimesPosts

Siyasa : Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Jihar Kano (KANSIEC), ta sanya ranar Asabar 30 ga Oktobar 2027, domin gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin jihar.
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Jihar Kano (KANSIEC), ta sanya ranar Asabar 30 ga Oktobar 2027, domin gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin jihar. Timespots ta rawaito cewa, wannan na cikin sanarwar da…
Ay Abdullahi1 min read

NDC ta kori ɗan takararta a Borno kan zargin yiwa Atiku kamfen
NDC ta kori ɗan takararta a Borno kan zargin yiwa Atiku kamfenJam’iyyar NDC a jihar Borno ta kori ɗaya daga cikin ’yan takararta na majalisar dokokin jihar, Mohammed Bunu, bisa zargin yi wa ɗan…
Ay Abdullahi1 min read

NDC ta bukaci INEC ta binciki ma'aikaciyar hukumar kan zargin sauya rahoton zaɓen fidda gwani a Kano
NDC ta bukaci INEC ta binciki ma'aikaciyar hukumar kan zargin sauya rahoton zaɓen fidda gwani a KanoJam’iyyar NDC reshen jihar Kano, ta bukaci hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta gudanar…
Ay Abdullahi2 min read