DA DUMI-DUMI: Gwamnatin tarayya ta sanar da rage farashin man fetur
DA DUMI-DUMI: Gwamnatin tarayya ta sanar da rage farashin man fetur Gwamnatin tarayya ta sanar da shirin rage farashin man fetur da ake sayarwa a gidajen mai na Kamfanin mai na kasa (NNPC) na tsawon…
Ay Abdullahi · Admin
· 1 min read

DA DUMI-DUMI: Gwamnatin tarayya ta sanar da rage farashin man fetur
Gwamnatin tarayya ta sanar da shirin rage farashin man fetur da ake sayarwa a gidajen mai na Kamfanin mai na kasa (NNPC) na tsawon kwanaki 30.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, Ministan Kuɗi kuma Ministan da ke Kula da tattalin aziƙin kasa, Taiwo Oyedele, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja ranar Alhamis.
Oyedele ya ce za a samu rangwame kan farashin fetur a gidajen mai na NNPC na tsawon wata guda, inda za a bai wa masu motocin jigilar fasinjoji fifiko.
Ya ce: “Za a samu rangwame kan fetur a NNPC na tsawon kwanaki 30, tare da bai wa masu harkar jigilar jama’a fifiko.”
Ministan ya kuma bayyana cewa gwamnatin tarayya ta cimma matsaya kan sabon farashin saukar da man fetur (landing cost), wanda za a rika duba shi duk wata.
Ya ce matakan na daga cikin ƙoƙarin gwamnati na rage wa ’yan Najeriya nauyin tsadar man fetur, musamman masu zirga-zirgar jama’a da fasinjoji.
More from TimesPosts

Siyasa Duniya A Yau Ko Kunsan Da Gabas Ta Tsakiya ke chiki
Da Dumi-Duminsa:Iran za ta ƙara nisan zangon makamanta masu linzami Zuwa Kilomita 1000 bayan Sojin Amurka Sun Sake Sansani a Tekun IndiaWani kakakin sojojin Iran, Mohammad Akraminia, ya bayyana cewa…
Ay Abdullahi1 min read

Siyasa Arewachin Nigeria Shin Haka Da gaskene
Matsaloli Goma da Suke Gaban Abba Kabir Yusuf a Zaben 2027.1. Karfin Kwankwasiyya da Kwankwaso2. Rashin sakin jiki da yan tsohuwar APC.3. Masu yiwa Kwankwasiyya aiki acikin gwamantin shi.4. Rashin…
Ay Abdullahi1 min read

Yadda ake daura Nmap a Android
Yadda ake daura Nmap a AndroidKa install Termux daga F-Droid ko official source.Buɗe Termux.Rubuta:pkg update pkg upgrade pkg install nmap Bayan an gama, ka tabbatar da installation:nmap --version…
Ay Abdullahi1 min read