Skip to content
TimesPosts homeTimesPostsThe record, as it happens.

Gwamnatin tarayya ta tsara ware Naira biliyan 84.48 domin aiwatar da shirin kawo ƙarshen auren ƙananan yara a Najeriya nan da shekarar 2030.

Gwamnatin tarayya ta tsara ware Naira biliyan 84.48 domin aiwatar da shirin kawo ƙarshen auren ƙananan yara a Najeriya nan da shekarar 2030.Ministar harkokin mata da ci gaban al’umma, Imaan…

Ay Abdullahi · Admin

· 1 min read

Gwamnatin tarayya ta tsara ware Naira biliyan 84.48 domin aiwatar da shirin kawo ƙarshen auren ƙananan yara a Najeriya nan da shekarar 2030.

Ministar harkokin mata da ci gaban al’umma, Imaan Sulaiman-Ibrahim, ce ta bayyana hakan a ranar Talata yayin bikin Ranar Ƙaramar Yarinya ta Duniya ta 2026 da ƙaddamar da dabarun yaƙi da auren ƙananan yara na shiyyar Arewa maso Yamma a Kano.

Ministar ta ce shirin na shekarar 2025 zuwa 2030 zai mayar da hankali wajen magance matsalolin da ke haddasa auren ƙananan yara, ciki har da talauci, rashin tsaro, hana ’yan mata zuwa makaranta da wasu al’adu masu illa.

Ta bayyana cewa an kiyasta kuɗin aiwatar da shirin na tsawon shekaru biyar zai kai Naira biliyan 140.8, inda gwamnatin tarayya za ta samar da kashi 60 cikin 100, wato Naira biliyan 84.48, yayin da abokan hulɗar ci gaba za su bayar da sauran Naira biliyan 56.32.

More from TimesPosts

Gwamnatin tarayya ta tsara ware Naira biliyan 84.48 domin aiwatar da shirin kawo ƙarshen auren ƙananan yara a Najeriya nan da shekarar 2030. | TimesPosts