Skip to content
TimesPosts homeTimesPostsThe record, as it happens.

Health and services. ::: Wannan hoton kusan hyper-realistic image kenan na polycystic kidney disease, wani nau'in ciwon ƙoda ne na gado, dake bayyana daga sanda aka kai shekaru 31 a duniya, family

Wannan hoton kusan hyper-realistic image kenan na polycystic kidney disease, wani nau'in ciwon ƙoda ne na gado, dake bayyana daga sanda aka kai shekaru 31 a duniya, family yake bibiya saboda naƙasun…

Ay Abdullahi · Admin

· 1 min read

Wannan hoton kusan hyper-realistic image kenan na polycystic kidney disease, wani nau'in ciwon ƙoda ne na gado, dake bayyana daga sanda aka kai shekaru 31 a duniya, family yake bibiya saboda naƙasun wata ƙwayar halitta.

Ba'a warkesa sai de ai managing symptoms, sannan masu wannan larurar ba Good candidate na dashen ƙoda ba, domin matsalar shine; ko andasa itama lalacewa zatai, saboda abinda ke lalata ƙodar a jikinsu yake kuma babu damar rabuwa dashi, kusan ko ina yana nan a jika.

Wannan na daga cikin irin larurorin da ya dace kasan dasu a family ɗinku, zai yiwu aita mutuwa har arika yan gidan su wane basa daɗewa a duniya alhalin kwai abinda ke kasheku wanda za'a iya daqilesa amma rashin sani da daukar abu da muhimmanci ya hana.

Ko aure za ai don de ana ta fama da batun gwajin Genotypes, HIV da sauransu ne... Amma sanin tarihin lafiyar family nada muhimmanci, shiyasa cikin fararen fata har genetics testing suke.

Sannan wasu lokuta gujewa auren dangi alkhairi ne, domin in akwai wata cutar dake farautarku idan kukaita hayyafa tsakaninku ana hada aure tohfa abin zai muni, tun cutar bata bayyana sosai ba gaba zata fito fili, a Sannan ne za'a gane kuskuren, shiyasa kabilu da dama basa auren dangi.

Ibrahim Yakubu Yusuf

More from TimesPosts