Ina Mafita Manya Arewachin Nigeria. :::: MANYAN AREWA SU KAWO DAUKI
MANYAN AREWA SU KAWO DAUKIBatun Hajiya Zainab 'yar Maigirma Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wacce take auren Maigirma Gwamnan jihar Kano Engr Abba Kabir Yusuf... Wallahi har ni, ina daga cikin wadanda…
Ay Abdullahi · Admin
· 2 min read

MANYAN AREWA SU KAWO DAUKI
Batun Hajiya Zainab 'yar Maigirma Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wacce take auren Maigirma Gwamnan jihar Kano Engr Abba Kabir Yusuf...
Wallahi har ni, ina daga cikin wadanda suke daukar cewa rabuwar Kwankwaso da Gwamna Abba a siyasa shirin fim ne kawai, tsara wa sukayi, to amma batun Hajiya Zainab da ta kai karan mijinta Gwamna Abba Kabir Kotu don a raba aurensu, ya canza min tunani
A yanzu na samu gamsuwa dari bisa dari Kwankwaso da Abba Kabir sun rabu, kuma rabuwa mummuna, tunda har ya fara shafan iyalansu
Matar aure da yaranta guda shida bayan sun shekara 21 suna zaman aure, ta kai kara Kotu zata nemi saki, kuma kar a manta, akwai yaron Kwankwaso ya ajiye mukamin kwamishina a Gwamnatin Abba, wannan yana bayyana girman al'amarin
To amma, a dayan bangare, wannan rabuwa ta siyasa tsakanin Kwankwaso da Gwamna Abba masifa ce, yana kara bayyana mana cewa yanzu a Arewa bamu da wani babban Mutum da ya rage wanda zai iya bada umarni, ya zartar da hukunci a bi, ba tare da gardama ba
Amma duk da haka, muna jaddada kira ga Manyan Arewa (Sarakuna da Malamai), ku shiga lamarin Kwankwaso da Abba, musamman sha'anin auren Abba da Matarsa 'yar Kwankwaso wacce take neman sakin aure a Kotu
A fa cire maganar siyasa, domin wannan abin fa idan aka barshi ya kai inda ba'a so, to tabbas zai haifar da abubuwa marassa dadi a yankin Arewacin Nigeria, kuma kar a manta mu Musulmai ne ba maguzawa ba
Idan manyan Arewa basu tashi ba, abin nan zai iya haifar da mummunar gaba, tarwatsewar dangi, domin a cikin zuriyar Kwankwaso da Gwamna Abba za'a koma Ɗa yana gaba da Kawunsa, ko Uba yana gaba da Ɗan uwansa
A bangaren siyasa kuma, wannan zai kara rura wutar rikicin siyasa da adawa na rashin hankali a jihar Kano, ya kamata Manyan Arewa Sarakuna da Malamai su shiga cikin wannan maganar ba tare da bata lokaci ba, domin duk abinda ya taba Kano to ya taba jihohin Arewa
Muna rokon Allah Ya sasanta tsakanin su
More from TimesPosts

Siyasa Nigeria A Yau ::: Mai Yayi Zafi Haka kuwa
Matar Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, mai suna Zainab Musa Kwankwaso, ta shigar da ƙarar neman raba aurenta da gwamnan a wata kotun Upper Area Court da ke Gudu, a birnin Abuja, inda ta kuma…
Ay Abdullahi1 min read

Siyasa Nigeria A Yau ::: Obi da magoya bayan NDC sun yi watsi da sabon taken Najeriya da Tinubu ya dawo da shi
Obi da magoya bayan NDC sun yi watsi da sabon taken Najeriya da Tinubu ya dawo da shi Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, tare da magoya bayan jam’iyyar, sun yi watsi da sabon…
Ay Abdullahi1 min read

Siyasa. INEC za ta yi biyayya ga hukuncin kotu kan cancantar Atiku a zaɓen 2027 – Amupitan
INEC za ta yi biyayya ga hukuncin kotu kan cancantar Atiku a zaɓen 2027 – AmupitanHukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta ce za ta yi biyayya ga duk wani hukuncin kotu kan cancantar tsohon…
Ay Abdullahi1 min read