Labaran Duniya :: DA DUMI DUMI. Magoya bayan jam’iyyun Larabawa mafiya yawa musulmai da ke Isra’ila na murnar sakamakon zaɓen farko, yayin da hasashen sakamakon zaɓe ya nuna cewa jam’iyyun
DA DUMI DUMI. Magoya bayan jam’iyyun Larabawa mafiya yawa musulmai da ke Isra’ila na murnar sakamakon zaɓen farko, yayin da hasashen sakamakon zaɓe ya nuna cewa jam’iyyun za su samu ƙarin kujeru.Ana…
Ay Abdullahi · Admin
· 1 min read

DA DUMI DUMI.
Magoya bayan jam’iyyun Larabawa mafiya yawa musulmai da ke Isra’ila na murnar sakamakon zaɓen farko, yayin da hasashen sakamakon zaɓe ya nuna cewa jam’iyyun za su samu ƙarin kujeru.
Ana hasashen cewa jam’iyyun biyu za su samu kujeru tsakanin 17 zuwa 18 a majalisar dokokin Isra’ila.
Zakuyi mamaki idan nace muku akwai musulmai dake cikin isra'ila ba Larabawa sun kai kusan kashi 21% na al’ummar Isra’ila, wato kusan mutum ɗaya cikin biyar.
Yawancinsu Falasɗinawa ne waɗanda suka ci gaba da zama a yankunan da suka zama Isra’ila bayan yaƙin 1948, tare da zuriyarsu.
Mafi yawansu Musulmai ne, amma akwai Kiristoci da kuma Larabawa mabiya addinin Druze.
Yawancinsu suna da izinin zama ɗan ƙasar Isra’ila, suna iya zaɓe da tsayawa takarar kujerun majalisa.
Suna zaune a garuruwa kamar Nazareth, Umm al-Fahm da wasu yankunan Galili.
Wasu suna shiga siyasar Isra’ila domin kare haƙƙoƙinsu, yayin da wasu ke adawa da manufofin gwamnatin Isra’ila, musamman game da Falasɗinawa da Gaza.
Wannan ma nasara ce ga mu$ulman duniya
Alhamdulillah
More from TimesPosts

Wannan hoton plain radiographic scan ne na jiki, ku kalli tarin ƙibar ta gefe da gefe, sannan daga tsakiya kuma kalli ƙashinta ka gani. Huhun a takure yake, sannan kashin gadon bayar
Wannan hoton plain radiographic scan ne na jiki, ku kalli tarin ƙibar ta gefe da gefe, sannan daga tsakiya kuma kalli ƙashinta ka gani. Huhun a takure yake, sannan kashin gadon bayar ya zaizaye…
Ay Abdullahi2 min read

Labaran Duniya :: Tsuntsu Mai wayyo...
Wannan Mata me Suna Aisha Ahmad Abdullahi yar asalin Jahar Niger State ce Amma tana Aure a Kaduna Road inka wuce Dutsen Zuba ta Kirki Wani kasuwanci ita da Mijinta Wanda sukai inviting na Mutane da…
Ay Abdullahi2 min read

Labaran Duniya ::: YAYI SHIRME SHIMA
YAYI SHIRME SHIMA.Kylian Mbappé ya fuskanci suka a China bayan da ya kira wani hoton barkwanci (meme) na Mao Zedong da ke nuna shi a matsayin wani azzalumin shugaban China.Real Madrid ta nemi a fuwa…
Ay Abdullahi1 min read