Labaran siyasa ::: Rikicin APC: Dan takara ya shigar da ƙara ga NEC da hukumomin tsaro
Rikicin APC: Dan takara ya shigar da ƙara ga NEC da hukumomin tsaroRikicin da ke cikin jam’iyyar APC a jihar Zamfara ya sake ɗaukar sabon salo, biyo bayan ƙorafin da wani dan takara Hassan Umar…
Ay Abdullahi · Admin
· 1 min read

Rikicin APC: Dan takara ya shigar da ƙara ga NEC da hukumomin tsaro
Rikicin da ke cikin jam’iyyar APC a jihar Zamfara ya sake ɗaukar sabon salo, biyo bayan ƙorafin da wani dan takara Hassan Umar Dangaladima ya shigar gaban kwamitin zartarwa na ƙasa (NEC) da kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) na jam’iyyar, da kuma hukumomin tsaro.
Dan takarar ya shigar da ƙorafin ne kan yadda aka tsara kwamitin da zai gudanar da sabon zaɓen fitar da gwani, wanda kotu ta bayar da umarnin a sake gudanarwa.
Wannan zaɓen fitar da gwani dai na mazabar tarayya ta Kaura Namoda/Birnin Magaji ne, biyo bayan umarnin da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta bayar.
Dangaladima ya zargi shugaban jam’iyyar na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, da kafa kwamitin gudanar da zaɓen shi kaɗai, ba tare da tuntubar kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) ba.
Ya yi zargin cewa yadda aka tsara kwamitin ya haifar da shakku kan ko zai gudanar da zaɓen cikin adalci da rashin nuna son kai. Saboda haka, ya buƙaci shugabannin jam’iyyar da su sake duba tsarin kafa kwamitin kafin gudanar da sabon zaɓen fitar da gwani.
A cikin ƙorafin nasa, Dangaladima ya yi iƙirarin cewa ba a taɓa gudanar da taron kwamitin NWC domin tattaunawa ko amincewa da waɗanda aka naɗa cikin kwamitin ba.
Haka kuma, ya ce ba a tuntubi masu neman takarar, da shugabancin jam’iyyar APC na jihar Zamfara, da sauran masu ruwa da tsaki kafin kafa kwamitin ba.
Sai dai, shugaban jam’iyyar, Yilwatda, ta bakin mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai da sadarwa, Abimbola Tooki, ya yi watsi da zarge-zargen, inda ya bayyana su a matsayin maras tushe.
More from TimesPosts

Siyasa Nigeria. :: ADC ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin babbar kotun tarayya na soke takarar Atiku
ADC ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin babbar kotun tarayya na soke takarar Atiku Jam’iyyar ADC ta ce ta shigar da ƙara a Kotun Ɗaukaka Ƙara kan hukuncin da Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke a…
Ay Abdullahi2 min read

Dalilin da ya mu ka ƙara yawan rumfnunan zaɓe - INEC
Dalilin da ya mu ka ƙara yawan rumfnunan zaɓe - INECHukumar zaɓe ta INEC ta ce ƙarin da aka samu na wasu rumfunan zaɓe sun samo asali ne daga hukuncin kotu da ya haifar da ƙirƙirar sabbin mazaɓu a…
Ay Abdullahi1 min read

Siyasa ::: Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da lambar da za a nemi rancen kuɗi da kayan abinci da na amfanin gida ta wayar hannu
Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da lambar da za a nemi rancen kuɗi da kayan abinci da na amfanin gida ta wayar hannuGwamnatin Tarayyar ta ƙaddamar da wani sabon tsarin bada rancen kuɗi ta hanyar amfani…
Ay Abdullahi1 min read