Labaran Siyasa ::: Siyasa Nigeria ADC ba ta shiryawa zaɓen 2027 ba - Dalung
ADC ba ta shiryawa zaɓen 2027 ba - Dalung Tsohon ministan Matasa da Wasanni, Solomon Dalung, ya zargi Sakataren Jam’iyyar ADC na ƙasa, Rauf Aregbesola, da naɗa shugabannin kwamitocin riƙon ƙwarya a…
Ay Abdullahi · Admin
· 1 min read

ADC ba ta shiryawa zaɓen 2027 ba - Dalung
Tsohon ministan Matasa da Wasanni, Solomon Dalung, ya zargi Sakataren Jam’iyyar ADC na ƙasa, Rauf Aregbesola, da naɗa shugabannin kwamitocin riƙon ƙwarya a jihohi 36 ba tare da bin ƙa’ida ba.
Dalung ya ce matakin ya saɓa wa shari’ar da ke gaban Kotun Ƙoli, inda wasu daga cikin waɗanda aka naɗa ke ƙalubalantar hukuncin Kotunan Ɗaukaka Ƙara da suka cire su daga muƙamansu.
A cikin wani saƙon bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Talata, tsohon ministan ya bukaci shugabancin ADC da ya dakatar da rantsar da kwamitocin, wadda aka shirya gudanarwa ranar Laraba, har sai Kotun Ƙoli ta yanke hukunci.
Ya bayyana cewa naɗin da Aregbesola ya yi na iya zama tamkar raina hukuncin kotu da kuma yunƙurin riga-kafin hukuncin da Kotun Ƙoli za ta yanke.
Dalung ya kuma nuna damuwa kan yadda Aregbesola ya sanya hannu shi kaɗai a takardun naɗin, ba tare da sa hannun shugaban jam’iyyar na ƙasa ba, yana mai cewa ya kamata a bi tsarin gudanarwar jam’iyyar.
Ya yi gargaɗin cewa idan ADC ta ci gaba da rantsar da kwamitocin, hakan na iya kawo cikas ga shigar jam’iyyar zaɓen 2027.
“Idan jam’iyyar ta ci gaba da rantsar da waɗannan mutane, hakan na nuna cewa ADC ba ta da niyyar shiga zaɓen 2027,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa idan Kotun Ƙoli ta yanke hukunci a kan jam’iyyar, kada ta ɗora laifin kan wasu, domin abin da ya faru zai zama matsalar da ita da kanta ta jawo.
Dalung ya buƙaci shugabancin ADC da ya janye takardun naɗin tare da jiran hukuncin Kotun Ƙoli.
More from TimesPosts

Labaran siyasa ::: Rikicin APC: Dan takara ya shigar da ƙara ga NEC da hukumomin tsaro
Rikicin APC: Dan takara ya shigar da ƙara ga NEC da hukumomin tsaroRikicin da ke cikin jam’iyyar APC a jihar Zamfara ya sake ɗaukar sabon salo, biyo bayan ƙorafin da wani dan takara Hassan Umar…
Ay Abdullahi1 min read

Siyasa Nigeria. :: ADC ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin babbar kotun tarayya na soke takarar Atiku
ADC ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin babbar kotun tarayya na soke takarar Atiku Jam’iyyar ADC ta ce ta shigar da ƙara a Kotun Ɗaukaka Ƙara kan hukuncin da Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke a…
Ay Abdullahi2 min read

Dalilin da ya mu ka ƙara yawan rumfnunan zaɓe - INEC
Dalilin da ya mu ka ƙara yawan rumfnunan zaɓe - INECHukumar zaɓe ta INEC ta ce ƙarin da aka samu na wasu rumfunan zaɓe sun samo asali ne daga hukuncin kotu da ya haifar da ƙirƙirar sabbin mazaɓu a…
Ay Abdullahi1 min read