Skip to content
TimesPosts homeTimesPostsThe record, as it happens.

Labaran Wasani

🗞️ LABARI 💥 Ashley Young ya bayyana cewa Antonio Conte koci ne mai tsananin horo da ƙwazo, wanda ba ya daina magana ko ihu yayin wasa. Ya ce horon Conte yana ƙunshe da yawan gudu da wahala, kuma…

Ay Abdullahi · Admin

· 1 min read

🗞️ LABARI 💥 Ashley Young ya bayyana cewa Antonio Conte koci ne mai tsananin horo da ƙwazo, wanda ba ya daina magana ko ihu yayin wasa. Ya ce horon Conte yana ƙunshe da yawan gudu da wahala, kuma yana buƙatar ƴan wasa su kasance masu jajircewa.

Young ya kuma bayyana cewa tarukan nazarin wasa a ƙarƙashin Conte suna iya ɗaukar sa’o’i da dama, musamman bayan rashin nasara. A wasu lokuta, Conte kan dakatar da bidiyon akai-akai domin tambayar ƴan wasa dalilin ayyukan su, har wasu daga cikin ƴan wasan sukan gaji ko su fara bacci.

Saboda haka, Young ya yi gargaɗi cewa idan Manchester United ta naɗa Conte amma ƴan wasan ta ba sa son gudu da yin ƙoƙarin da yake buƙata, hakan na iya haifar da babban rikici ko mummunan sakamako.

Tushen labari:TNT sports,FC Inter 1908

More from TimesPosts