Muna fatan INEC za ta dawo da sunan Gwarzo cikin ’yan takarar gwamnan Kano - NDC
Muna fatan INEC za ta dawo da sunan Gwarzo cikin ’yan takarar gwamnan Kano - NDCJam’iyyar NDC a Jihar Kano ta bayyana fatan cewa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC) za ta dawo da sunan ɗan…
Ay Abdullahi · Admin
· 1 min read
Muna fatan INEC za ta dawo da sunan Gwarzo cikin ’yan takarar gwamnan Kano - NDC
Jam’iyyar NDC a Jihar Kano ta bayyana fatan cewa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC) za ta dawo da sunan ɗan takararta na gwamna, Aminu Abdussalam Gwarzo, da mataimakinsa cikin jerin ’yan takarar zaɓen gwamnan jihar na 2027, idan aka gano cewa kuskure ne aka yi wajen cire sunayensu.
Shugaban jam’iyyar na jihar Kano, Hussaini Isah Mai Riga, ne ya bayyana hakan, inda ya ce jam’iyyar ta kai ƙorafinta ga uwar jam’iyya ta ƙasa, wadda ita ma ta miƙa batun ga INEC.
Mai Riga ya ce hukumar zaɓen ta yi alƙawarin gudanar da bincike kan cire sunayen ’yan takarar, yayin da jam’iyyar ke jiran sakamakon binciken.
“Mun rubuta wa uwar jam’iyyarmu ta ƙasa, ita kuma ta miƙa batun ga INEC. Hukumar ta ce za ta gudanar da bincike, kuma idan aka gano kuskure ne, za ta dawo da matsayin ’yan takararmu,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa a halin yanzu jam’iyyar na jiran martanin hukumar kafin ta yanke shawarar matakin da za ta ɗauka na gaba.
An cire sunayen Gwarzo da mataimakinsa daga jerin sunayen ’yan takarar gwamnan Kano na ƙarshe da INEC ta fitar, lamarin da ya jawo damuwa kan yiwuwar jam’iyyar ta shiga zaɓen gwamnan jihar na 2027.
Yanzu haka NDC na jiran sakamakon binciken hukumar zaɓen domin tabbatar da matsayin ’yan takararta da kuma sanin matakin da za ta ɗauka na gaba.
More from TimesPosts

Alleged ₦110.4bn kogi Fraud: Witness Says ₦1.425bn Was Used for Forex Transactions in Two Months
Alleged ₦110.4bn kogi Fraud: Witness Says ₦1.425bn Was Used for Forex Transactions in Two MonthsA prosecution witness in the ongoing trial of former Kogi State Governor, Yahaya Bello has told the…
Ay Abdullahi3 min read

LABARI 💥 Alejandro Garnacho na ƙoƙarin ganin ya koma ɗan wasan Aston Villa na dindindin, bayan ya koma ƙungiyar a matsayin aro daga Chelsea.
LABARI 💥 Alejandro Garnacho na ƙoƙarin ganin ya koma ɗan wasan Aston Villa na dindindin, bayan ya koma ƙungiyar a matsayin aro daga Chelsea. Yarjejeniyar aro ta ƙunshi damar sayen ɗan wasan na…
Ay Abdullahi1 min read

LABARI 💥 CRISTIANO RONALDO NA ƘARA NISANTA DA KOMAWA TAWAGAR PORTUGAL.
🗞️ LABARI 💥 CRISTIANO RONALDO NA ƘARA NISANTA DA KOMAWA TAWAGAR PORTUGAL.A cewar ƴar uwar sa Elma Aveiro, yiwuwar Cristiano Ronaldo ya sake bugawa tawagar ƙasar Portugal wasa na ƙara raguwa.Elma ta…
Ay Abdullahi1 min read