NDC ta bukaci INEC ta binciki ma'aikaciyar hukumar kan zargin sauya rahoton zaɓen fidda gwani a Kano
NDC ta bukaci INEC ta binciki ma'aikaciyar hukumar kan zargin sauya rahoton zaɓen fidda gwani a KanoJam’iyyar NDC reshen jihar Kano, ta bukaci hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta gudanar…
Ay Abdullahi · Admin
· 2 min read

NDC ta bukaci INEC ta binciki ma'aikaciyar hukumar kan zargin sauya rahoton zaɓen fidda gwani a Kano
Jam’iyyar NDC reshen jihar Kano, ta bukaci hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta gudanar da bincike kan zargin fitar da rahotannin sa-ido daban-daban masu saɓani da juna da kuma marasa kwanan wata game da zaɓen fidda gwani na jam’iyyar a jihar.
Jam’iyyar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa mai kwanan wata 19 ga Oktoba, wadda babban lauya Magaji Mato Ibrahim, SAN, tare da wasu lauyoyi huɗu suka sanya wa hannu.
Sanarwar ta mayar da martani ne ga wata sanarwa da lauyoyin Bola Aidi, SAN & Co., suka fitar a ranar 17 ga Oktoba, domin kare wasu mutum biyar da ke ikirarin cewa su ne ’yan takarar NDC a Kano.
A baya-bayan nan, wasu mambobin tafiyar Kwankwasiyya a cikin NDC sun miƙa ƙorafi a hedikwatar INEC da ke Kano, inda suka zargi shugabar sashen zaɓe da sa-ido kan jam’iyyun siyasa ta hukumar a jihar, Hauwa Buhari, da yin zargin yin katsalandan ga ainihin bayanan zaɓen fidda gwani na jam’iyyar.
A martaninsu, lauyoyin NDC sun ce ƙorafin ya fito ne bisa umarnin shugabancin jam’iyyar na jihar Kano, suna mai cewa jam’iyyar na da haƙƙin ƙalubalantar sahihancin bayanan hukuma da ake zargin sun nuna sakamakon zaɓen fidda gwani nata.
Sun bayyana cewa rahotannin da jami’ar ta sanya wa hannu sun ƙunshi bayanai masu saɓani, inda wasu ba su da kwanan wata, yayin da aka saka sunayen wasu mutanen da jam’iyyar ba ta tantance ko amincewa da takararsu ba.
A cewar lauyoyin, an kuma cire sunayen wasu sahihan ’yan takara da aka bayyana a cikin fom ɗin EC9D, wanda shugaban jam’iyyar na ƙasa da sakatarenta suka sanya wa hannu, da kuma jerin sunayen da aka miƙa wa INEC.
Lauyoyin sun ƙara da cewa ana zargin jami’ar ta amince da akwai kura-kurai a rahoton, sannan aka aika da wani gyararren rahoto zuwa hedikwatar INEC ta ƙasa, ba tare da an sanar da matakan aiwatar da gyaran ba.
Sun ce waɗannan zarge-zarge sun isa su sa hukumar ta gudanar da bincike na cikin gida tare da gyara bayananta, ba tare da jiran sakamakon shari’a ba.
Haka kuma, lauyoyin sun zargi mutanen biyar da shigar da ƙara a Babbar Kotun Tarayya ta hannun lauyoyin Bola Aidi ba tare da sanar da sahihan ’yan takarar jam’iyyar da lamarin ya shafa ba sai a baya-bayan nan.
Sun ce rashin haɗa waɗanda abin ya shafa a shari’ar tun farko ya sabawa ƙa’idojin sauraron ɓangarorin da abin ya shafa domin tabbatar da adalci.
Lauyoyin sun kuma jaddada cewa bayanan jam’iyyar, ciki har da fom ɗin EC9D da takardun tantance ’yan takara, sun nuna cewa mutanen da lauyoyin Bola Aidi ke wakilta ba su cika sharuddan tsayawa takara ba.
More from TimesPosts

Obi ya bukaci ’yan Najeriya mazauna ƙasashen waje su daina turo kuɗi gida
Obi ya bukaci ’yan Najeriya mazauna ƙasashen waje su daina turo kuɗi gidaPeter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, ya bukaci ’yan Najeriya mazauna Birtaniya da su sake duba yadda suke…
Ay Abdullahi1 min read

Za mu dawo da tallafin man fetur - Kwankwaso
Za mu dawo da tallafin man fetur - Kwankwaso Mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce jam’iyyar za ta ɗauki duk matakan da suka dace, ciki har da dawo da…
Ay Abdullahi1 min read

WAI SHIN MAINE GASKIYA WANNA MAGANA : El-Rufai Yayi Yunkurin Bawa Jamian EFCC Cin Hancin Dala Dubu Dari Shida - a Cewar Shedan SSS a Kotu
El-Rufai Yayi Yunkurin Bawa Jamian EFCC Cin Hancin Dala Dubu Dari Shida - a Cewar Shedan SSS a KotuWani mai binciken laifuka na hukumar tsaro ta farin kaya (SSS) ya bayyana a gaban kotu cewa tsohon…
Ay Abdullahi1 min read