Skip to content
TimesPosts homeTimesPostsThe record, as it happens.

NDC ta kori ɗan takararta a Borno kan zargin yiwa Atiku kamfen

NDC ta kori ɗan takararta a Borno kan zargin yiwa Atiku kamfenJam’iyyar NDC a jihar Borno ta kori ɗaya daga cikin ’yan takararta na majalisar dokokin jihar, Mohammed Bunu, bisa zargin yi wa ɗan…

Ay Abdullahi · Admin

· 1 min read

NDC ta kori ɗan takararta a Borno kan zargin yiwa Atiku kamfen

Jam’iyyar NDC a jihar Borno ta kori ɗaya daga cikin ’yan takararta na majalisar dokokin jihar, Mohammed Bunu, bisa zargin yi wa ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, Atiku Abubakar, kamfen.

A cikin wata wasiƙa mai kwanan wata 25 ga Oktoba, 2026, jam’iyyar ta ce matakin ya biyo bayan gano wasu kayan kamfe da ke ɗauke da tambarin ADC, hoton Atiku da kuma sunan Bunu.

Mataimakin shugaban NDC na jihar, Umar Fema, ya bayyana cewa an fara binciken ne daga matakin shugabancin mazabar Hausari, kafin a miƙa batun ga shugabancin jam’iyyar na ƙaramar hukumar Maiduguri Metropolitan Council domin zurfafa bincike.

A cewar wasiƙar, an gayyaci Bunu sau biyu, a ranakun 23 da 24 ga Oktoba, domin ya kare kansa kan zargin, amma bai halarci zaman binciken ba.

Bayan nazarin rahoton kwamitin binciken, shugabancin jam’iyyar ya amince da shawarar korarsa, tare da miƙa matakin ga shugabancin NDC na jihar.

Sai dai jam’iyyar ta bayyana cewa batun cire Bunu daga matsayin ɗan takara ya bambanta da batun dakatarwa ko korarsa daga cikakken zama ɗan jam’iyyar, wanda ke buƙatar bin ƙa’idojin kundin tsarin jam’iyyar.

More from TimesPosts

NDC ta kori ɗan takararta a Borno kan zargin yiwa Atiku kamfen | TimesPosts