Skip to content
TimesPosts homeTimesPostsThe record, as it happens.

Obi ya bukaci ’yan Najeriya mazauna ƙasashen waje su daina turo kuɗi gida

Obi ya bukaci ’yan Najeriya mazauna ƙasashen waje su daina turo kuɗi gidaPeter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, ya bukaci ’yan Najeriya mazauna Birtaniya da su sake duba yadda suke…

Ay Abdullahi · Admin

· 1 min read

Obi ya bukaci ’yan Najeriya mazauna ƙasashen waje su daina turo kuɗi gida

Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, ya bukaci ’yan Najeriya mazauna Birtaniya da su sake duba yadda suke tura kuɗi ga ’yan uwa da sauran mutanen da ke neman taimakon kuɗi a gida.

Obi ya bayyana hakan ne yayin wani taron tattaunawa da magoya bayansa mazauna ƙasashen waje a Manchester, Birtaniya, inda ya ce taimakon kuɗi ba ya magance tushen matsalolin tattalin arzikin Najeriya.

Ya ce matsalolin ƙasar na da alaƙa da rashin ingantaccen shugabanci, yana mai cewa ci gaba da aika kuɗi na iya rage wa iyalai wahala na ɗan lokaci, amma ba zai magance matsalolin da ke jefa su cikin talauci ba.

“Idan kuna da mutanen da ke neman kuɗi a Najeriya a yanzu, ku gaya musu a’a,” in ji Obi.

Tsohon gwamnan jihar Anambra ya kuma bukaci ’yan Najeriya mazauna ƙasashen waje da su yi amfani da hulɗarsu da ’yan uwa wajen wayar da kansu kan muhimmancin zaɓen shugabannin da za su inganta tattalin arziki da tabbatar da kyakkyawan shugabanci.

Obi ya ce a lokacin da yake gwamnan Anambra, ya ba da fifiko wajen tara kuɗaɗen gwamnati da sarrafa su yadda ya kamata.

Ya kuma yi kira ga ’yan Najeriya da su fara sauyi ta hanyar zaɓen shugabannin da ake ganin ba su da yawan cin hanci da rashawa.

Ya bukaci ’yan ƙasar da su ɗauki babban zaɓen 2027 da muhimmanci, yana mai cewa zaɓen zai taka muhimmiyar rawa wajen tantance makomar Najeriya.

Obi ya jaddada cewa inganta ƙasar na buƙatar ’yan ƙasa su riƙa neman shugabanci na gari, bin diddigin ayyukan shugabanni da kuma zaɓen waɗanda ke da nagarta da ƙwarewar tafiyar da al’amuran ƙasa.

More from TimesPosts