Skip to content
TimesPosts homeTimesPostsThe record, as it happens.

Shekaru 179 da suka wuce wato a shekarar 1847 kafin a sami allurar anaesthesia dake ɗauke zafi ko sanya bacci in za ai tiyata, sau tari saukin azaba ya ta'allaka

Shekaru 179 da suka wuce wato a shekarar 1847 kafin a sami allurar anaesthesia dake ɗauke zafi ko sanya bacci in za ai tiyata, sau tari saukin azaba ya ta'allaka ne da saurin da likita yayi wajen…

Ay Abdullahi · Admin

· 1 min read

Shekaru 179 da suka wuce wato a shekarar 1847 kafin a sami allurar anaesthesia dake ɗauke zafi ko sanya bacci in za ai tiyata, sau tari saukin azaba ya ta'allaka ne da saurin da likita yayi wajen yakewa ko cire wani abu, gwargwadon jinkirin da aka samu gwargwadon ihun da mutum zai.

Likitan fiɗa Dr. Robert ya kafa tarihi inda yai tiyatar yanke ƙafa wato amputation cikin sekonni 25 kacal, saide saurin yazo da matsala domin saida ya haɗa da gutsire yatsun likitan dake taimaka masa, inda a ƙarshe da mara lafiyan da aka cirewa ƙafar da shi likitan da yake riƙe da ƙaffar har aka haɗa da yatsunsa duk suka mutu dalilin shigar kwayoyin cuta ta cikin jini wato Sepsis.... Ɗaya attendance kuma dake sanya ido shima nan ya yanke jiki ya faɗi a sume ganin firgicin cire kafa da yatsun abokin aiki, inda suman yazo da ƙarar kwana shima ya mutu.

A takaice de mutum uku sun mutu, tiyata daya tilo wacce ta janyo mortality rate ya kai 300%.

Tun daga nan aka qara fadada binkicen nemo allurar kashe zafi. Alhamdulillah yanzu labari ya canza. Me kuke tunani inda ba allurar kashe zafi, ace za'ai CS a ciro ɗa haka kamar yadda aka rika yi a b

aya?

More from TimesPosts