Skip to content
TimesPosts homeTimesPostsThe record, as it happens.

Siyasa A Yau :::: BUƊAƊƊIYAR WASIKA ZUWA GA MAI GIRMA GWAMNAN JIHAR KANO, INJINIYA Abba Kabir Yusuf.

BUƊAƊƊIYAR WASIKA ZUWA GA MAI GIRMA GWAMNAN JIHAR KANO, INJINIYA Abba Kabir Yusuf.Take: Mulki amanar jama'a ne, amma mutunci da kyakkyawar mu'amala su ne ginshiƙin shugabanci.Mai girma Gwamna Abba…

Ay Abdullahi · Admin

· 3 min read

BUƊAƊƊIYAR WASIKA ZUWA GA MAI GIRMA GWAMNAN JIHAR KANO, INJINIYA Abba Kabir Yusuf.

Take: Mulki amanar jama'a ne, amma mutunci da kyakkyawar mu'amala su ne ginshiƙin shugabanci.

Mai girma Gwamna Abba Kabir Yusuf,

Da girmamawa da kuma kishin ci gaban jihar Kano, na ke ganin ya dace in yi maka wasu shawarwari bisa la'akari da kalaman da ka yi a wajen taron da aka gudanar a gidan gwamnatin Kano a yau Litinin.

Da farko, ya kamata ka fahimci cewa kai ba kawai miji ba ne, kai ne jagoran al'ummar Kano, kuma mutane da dama su na kallon yadda ka ke gudanar da harkokinka na yau da kullum a matsayin abin koyi.

1. Duk da cewa kai gwamna ne, kana da haƙƙin fuskantar matsalolin rayuwar aure kamar kowane ɗan Adam. Amma bai kamata matsalar da ta shafi rayuwar iyalinka ta zama wani dandali na furta kalaman da za su iya rage darajar ɗayan ɓangaren ba. Abubuwan da su ka shafi aure sun fi dacewa a warware su cikin sirri, hikima da mutunta juna.

2. Ya kamata a ce ka kiyaye mutuncin matar da ka zauna da ita tsawon shekaru. Ko da aure ya kai ga ƙarshe, hakan bai kamata ya zama dalilin mantawa da mutuncin wanda ku ka taɓa gina rayuwa tare da shi ba. Mace ba ta rasa mutuncinta saboda neman rabuwa da mijinta. Haka kuma, rashin jituwar aure ba ya ba kowane ɓangare lasisin wulaƙanta ɗayan.

3. Ka guji kalaman da za su iya zama abin ɓata rai ko tozarta wani. Mai girma Gwamna, kalamai suna da nauyi, musamman idan sun fito daga bakin wanda ya ke riƙe da babban muƙamin gwamnati. Maganar da mutum zai iya furtawa cikin fushi na ɗan lokaci, za ta iya zama abin tunawa da shi na tsawon shekaru. Saboda haka, ya kamata ka riƙa auna kalamanka kafin furta su a bainar jama'a.

4. Ka yi la'akari da makomar 'ya'yanku. Akwai yara da wannan lamari ya shafa kai tsaye. Duk abin da ya faru tsakanin iyaye, bai kamata a manta da tasirinsa ga zukatan yara ba. Ka yi ƙoƙari ka kare martabar mahaifiyarsu a gabansu, domin girmama mahaifiyarsu ba yana nufin ka rage darajarka ba ne.

5. Jagoranci ba wai iya cin zaɓe ko riƙe madafun iko ba ne kawai. Ya na buƙatar haƙuri, hikima, natsuwa, iya sarrafa fushi da kuma mutunta ra'ayin wasu. Idan shugaba ya kasa sarrafa kalamansa a lokacin da yake cikin damuwa, hakan na iya shafar yadda jama'a suke kallon jagorancinsa.

6. Ka ba jama'ar Kano abin da suka zaɓe ka dominsa. Al'ummar Kano suna da matsaloli da dama da suke buƙatar kulawar gwamnati: tsadar rayuwa, rashin aikin yi, ilimi, lafiya, tsaro da samar da hanyoyin samun abin dogaro da kai. Ya kamata waɗannan batutuwa su kasance a sahun gaba na hankalinka maimakon barin al'amuran iyali su mamaye hankalin jama'a.

A ƘARSHE:

Mai girma Gwamna, ba wai ina yi maka wannan shawara ne don raini ba, ko kuma in goyi bayan wani ɓangare a cikin matsalar auranka ba. Ina yin haka ne saboda ganin darajar shugabanci da mutuncin al'ummar Kano.

Idan har lamarin ya kai ga rabuwar aure, a bari a warware shi cikin mutunci da bin ƙa'idojin addini da doka. Kada ka bari fushi ko maganganun jama'a su sa ka furta kalaman da za ka iya yin nadama a kansu nan gaba.

Ka tuna: Sakin aure ba shi ne ƙarshen mutunci ba, kuma riƙe aure ba shi ne ma'aunin darajar mutum ba. Abin da ya fi muhimmanci shi ne yadda aka gudanar da lamarin.

Ina fatan za ka ɗauki wannan shawara a matsayin kira na gyara, ba suka ta son zuciya ba.

Allah Ya ba ka hikimar shugabanci, ya shiryar da kai zuwa ga abin da ya fi alheri, ya kuma kiyaye mutuncin dukkan waɗanda wannan lamari ya shafa.

Na gode.

Ummu Abiha Tasiu

16-11-2026.

More from TimesPosts

Siyasa A Yau :::: BUƊAƊƊIYAR WASIKA ZUWA GA MAI GIRMA GWAMNAN JIHAR KANO, INJINIYA Abba Kabir Yusuf. | TimesPosts