Siyasa. INEC za ta yi biyayya ga hukuncin kotu kan cancantar Atiku a zaɓen 2027 – Amupitan
INEC za ta yi biyayya ga hukuncin kotu kan cancantar Atiku a zaɓen 2027 – AmupitanHukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta ce za ta yi biyayya ga duk wani hukuncin kotu kan cancantar tsohon…
Ay Abdullahi · Admin
· 1 min read

INEC za ta yi biyayya ga hukuncin kotu kan cancantar Atiku a zaɓen 2027 – Amupitan
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta ce za ta yi biyayya ga duk wani hukuncin kotu kan cancantar tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, na tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.
Shugaban hukumar, Farfesa Joash Amupitan, ya ce INEC ba za ta ɗauki matakin da ya saɓa wa ingantaccen hukuncin kotu ba.
Ya bayyana cewa hukumar ba za ta dogara da rahotannin kafafen yaɗa labarai ko bayanan da ake yaɗawa a shafukan sada zumunta wajen fassara hukuncin kotu ba, sai ta samu kwafin hukuncin da aka tabbatar (CTC) tare da nazarinsa da neman shawarar lauyoyinta.
“Ya zuwa yanzu, ban samu sahihin kwafin hukuncin Babbar Kotun Tarayya ba, domin ba ma ɗaukar mataki bisa abin da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta kawai,” in ji shi.
Hakan na zuwa ne bayan wata hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ƙarƙashin Mai Shari’a Peter Lifu, wanda ya soke shugabancin jam’iyyar ADC na tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark, tare da rushe matakan da shugabancin ya ɗauka tun ranar 29 ga Yuli, 2025.
Kotun ta kuma hana INEC amincewa da Mark, Rauf Aregbesola da sauran mambobin kwamitin gudanarwar jam’iyyar a matsayin shugabanninta.
Sai dai ADC ta ƙi amincewa da hukuncin, tana mai shirin ɗaukaka ƙara, yayin da lauyanta, Kalu Kalu, ya ce kotun ba ta bayar da umarnin soke takarar Atiku kai tsaye ba.
Atiku, wanda ya lashe tikitin takarar shugaban ƙasa na ADC a watan Mayun 2026, shi ma ya yi watsi da hukuncin tare da alƙawarin ƙalubalantarsa a kotu.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya zaɓi tsohon gwamnan Jihar Rivers, Rotimi Amaechi, a matsayin abokin takararsa.
More from TimesPosts

Labaran Siyasa ::: Siyasa Nigeria ADC ba ta shiryawa zaɓen 2027 ba - Dalung
ADC ba ta shiryawa zaɓen 2027 ba - Dalung Tsohon ministan Matasa da Wasanni, Solomon Dalung, ya zargi Sakataren Jam’iyyar ADC na ƙasa, Rauf Aregbesola, da naɗa shugabannin kwamitocin riƙon ƙwarya a…
Ay Abdullahi1 min read

Labaran siyasa ::: Rikicin APC: Dan takara ya shigar da ƙara ga NEC da hukumomin tsaro
Rikicin APC: Dan takara ya shigar da ƙara ga NEC da hukumomin tsaroRikicin da ke cikin jam’iyyar APC a jihar Zamfara ya sake ɗaukar sabon salo, biyo bayan ƙorafin da wani dan takara Hassan Umar…
Ay Abdullahi1 min read

Siyasa Nigeria. :: ADC ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin babbar kotun tarayya na soke takarar Atiku
ADC ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin babbar kotun tarayya na soke takarar Atiku Jam’iyyar ADC ta ce ta shigar da ƙara a Kotun Ɗaukaka Ƙara kan hukuncin da Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke a…
Ay Abdullahi2 min read