Skip to content
TimesPosts homeTimesPostsThe record, as it happens.

Siyasa Nigeria A Yau ::: BABU MAI MURNA DA FARUWAR HAKA SAI MUTUMIN BANZA

BABU MAI MURNA DA FARUWAR HAKA SAI MUTUMIN BANZAAbinda yake faruwa a jihar Kano cibiyar Arewa bai yiwa duk wani mai mutunci dadi ba, babu mai murna da faruwar haka sai mutumin banzaAmma waye babban…

Ay Abdullahi · Admin

· 2 min read

BABU MAI MURNA DA FARUWAR HAKA SAI MUTUMIN BANZA

Abinda yake faruwa a jihar Kano cibiyar Arewa bai yiwa duk wani mai mutunci dadi ba, babu mai murna da faruwar haka sai mutumin banza

Amma waye babban mai laifi?

Karanta rubutun har karshe zaka fahimci babban mai laifi

Da farko, har da ni, ban taba ganin Hajiya Zainab matar Gwamnan jihar Kano Engr Abba Kabir Yusuf wacce take 'yar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ba, sai da muka ga labarinta a manyan jaridu ta kai karan mijinta Kotu tana neman sakin aure

Duk wani mai mutunci zai yi tunani da wadannan tambayoyi guda biyu:

(1) Shin Hajiya Zainab bata da magabata ne?

(2) shin a Kotu aka daura auren Zainab da Abba shekaru 21 da suka wuce ko a gida?

Amsoshi shine tana da magabata, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso shine Mahaifinta, sannan amsa na biyu shine a gida aka daura mata aure da Abba Kabir ba Kotu ba

To me yasa da ta tashi neman saki sai ta tafi Kotu wanda tana da masaniyar cewa labarin zai fito ya yadu a duniya, zamu iya fahimtar cewa sun zabi tafiya Kotu ne domin su tozarta Gwamna Abba Kabir Yusuf

Duk uban da yake da iko a kan 'yar sa kuma yana raye ba zai taba barinta tayi haka ba, musamman kuwa tunda har akwai 'ya'ya guda shida da aka haifa a cikin auren mai tsawon shekaru 21

Ina fata yanzu kun fahimci waye babban mai laifi? ba kowa bane face Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wannan matsalar bata fi karfin ya maganceta ba, amma saboda wata boyayyar manufarsa ya bari har aka kawo wannan mataki na tozarci

Shi kuma Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya tashi rama tozarcin da aka masa, sai yazo kan dandalin siyasa ya bayyana wa duniya cewa ya saki matarsa 'yar tsohon Maigidansa Kwankwaso

Wato sun zabi zuwa Kotu domin su tozartashi, shi kuma ya mayar da martani a dandalin siyasa

Ina bamu shawara, a matsayin mu na Musulmi kar mu yi wasa da kyakkyawar akidah na Musulunci da kuma tarbiyya Islamiyyah, duk girman bokon Musulmi, matukar ya karantu a akidah kuma ya samu tarbiyya na addini to ba za'a taba ganin kwamacala da shirme a lamarinsa ba

Allah Ya kyauta

More from TimesPosts

Siyasa Nigeria A Yau ::: BABU MAI MURNA DA FARUWAR HAKA SAI MUTUMIN BANZA | TimesPosts