Siyasa Nigeria A Yau. ::: Gwamna ba da matarsa yake ba
Gwamna ba da matarsa yake ba Musulunci bai yarda kotu ta sake bayanan ma’aurata ga yan jaridu ba. Aure babban al’amari ne; sirri ne tsakanin ma’aurata, hukumomi da Allah. Jaridar da ta sake labarin…
Ay Abdullahi · Admin
· 2 min read

Gwamna ba da matarsa yake ba
Musulunci bai yarda kotu ta sake bayanan ma’aurata ga yan jaridu ba. Aure babban al’amari ne; sirri ne tsakanin ma’aurata, hukumomi da Allah.
Jaridar da ta sake labarin sakin dokar mallakar bayanai ta bi na kundin tsarin mulki. Amma a ina ta san an kai takardar neman saki kotu? Watakila bayanan sun zo ne bayan an kama wasu da su ka taimaki matar ta fice daga gidan gwamnati.
Ashe kenan ba a so ta fita daga gidan mijinta tun da har an saka mata takunkumi, amma ta fita neman yanci. Cikin takardun kotu na neman saki suna cewa ba ta jin dadin auren, samun kulawa, soyayya da natsuwa.
A kasar Hausa duk macen da ta je kotu neman saki ba da izinin mijinta ba ta nunawa duniya an zalunce ta, an take hakkinta, kuma hakan zai jawo a rika kallon mijinta azzalumi, ko kuma ya ki sake ta dan yana jin dadin cutar da ita.
Idan mun sa hankali sosai mun ajiye “emotion" dan mu yi magana ta adalci, za mu gane akwai soyayya mai karfi tsakaninsu, da ba soyayya ba za su haifi yaya shida cikin kunci ba.
Zuwa kotu neman hakki daidai ne, a al’ada zaman aure hakuri ne, a addini sulhu alheri ne. Matsalar aurensu a fili take, sai wanda ba shi da “experience” na aure da mutuwar aure sosai.
Gwamna ya ki sakin matarsa ne saboda yana son ta, ya sa an kama wadanda su ka sa ta bar gidansa. Ya fahimci ana ziga ta ta kashe aurenta, amma shi bai so saki ba dan wulakanta ta.
Sakon da ya isar mai kaushi kan mimbarin siyasa ba na matarsa bane, sako ne ga wadanda su ke ganin idan ba ita zai mutu, kuma idan ya sake ta sai me. Masu cewa maganganun siyasa ne ke bata mata rai kan iyayenta ba su da adalci, iyayen nata ne su ka koyar da shi, kuma kyan da ya gaji ubansa har ya zarce shi.
More from TimesPosts

Siyasa Nigeria A Yau. ::: Matsin rayuwa da yan Nijeriya ke ciki zai iya baiwa APC matsala a Arewa a zaɓe mai zuwa - Kawu Sumaila
Matsin rayuwa da yan Nijeriya ke ciki zai iya baiwa APC matsala a Arewa a zaɓe mai zuwa - Kawu SumailaSanatan Kano ta Kudu, Suleiman Kawu, ya ce jam’iyyar APC na fuskantar ƙalubale wajen samun goyon…
Ay Abdullahi2 min read

Siyasa Nigeria A Yau. :::: Mun biya Naira biliyan 37 na bashin ƴan fansho da mu ka gada - Gwamna Abba
Mun biya Naira biliyan 37 na bashin ƴan fansho da mu ka gada - Gwamna Abba Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ce gwamnatinsa ta biya Naira biliyan 37 daga cikin bashin fansho da giratuti da ta gada…
Ay Abdullahi1 min read

Shin Maine Gaskiya Magana Akan Gwammana Abba Kabir Yusuf. :::: GWAMA ABBA BAI SAKI MATARSA BA
GWAMA ABBA BAI SAKI MATARSA BANa sa kudi Naira Miliyon uku (₦3,000,000) duk wanda ya kawo min hujja cewa Maigirma Gwamnan jihar Kano Engr Abba Kabir Yusuf ya saki matarsa Hajiya Zainab zan bashi…
Ay Abdullahi1 min read