Siyasa Nigeria A Yau. :::: Gwamnan Kano ya furta wasu kalamai da ke nuni da sakin matarsa yar gidan Kwankwaso
Gwamnan Kano ya furta wasu kalamai da ke nuni da sakin matarsa yar gidan Kwankwaso Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya furta wasu kalamai da su ke nuni da cewa ya amince da sakin matar sa Zainab Musa…
Ay Abdullahi · Admin
· 1 min read

Gwamnan Kano ya furta wasu kalamai da ke nuni da sakin matarsa yar gidan Kwankwaso
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya furta wasu kalamai da su ke nuni da cewa ya amince da sakin matar sa Zainab Musa Kwankwaso, ’yar tsohon ubangidansa a siyasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
A kwanan nan ne dai DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa Zainab ta maka gwamna Abba a kotu, inda ta ke neman saki ta hanyar khul'i saboda rikicin zamantakewa da ke faruwa tsakanin su.
Sai dai a yayin taron biyan kuɗin ƴan fansho a fadar gwamnatin Kano a ranar Litinin, gwamnan ya furta wasu kalamai, inda ya nuna ya amince da zama mai mace ɗaya a yanzu, amma yana da niyyar sake aure nan gaba.
Ya kuma ce ya umurci Kwamishinan yaɗa labarai da ya sanya sanarwa a gidajen rediyo da kafafen sada zumunta domin gayyatar matan da ke sha’awar auren gwamnan.
Yusuf ya bayyana cewa ya ji daɗin matakin da ya ɗauka, tare da roƙon Allah Ya azurta shi da mutanen kirki a rayuwarsa.
Hakan na zuwa ne bayan Zainab Musa Kwankwaso ta shigar da ƙarar neman raba aurensu a babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke Gudu, Abuja, ranar Asabar.
Takardar sammaci mai lamba CV/97/26 ta umarci gwamnan da ya gurfana a gaban kotun ranar 17 ga Nuwamba, 2026.
Abba Yusuf da Zainab sun yi aure ne a ranar 29 ga Yulin 2006, lokacin da gwamnan ke aiki a matsayin hadimi ga mahaifinta, Sanata Rabiu Kwankwaso, kuma aurensu ya haifar da ’ya’ya shida.
More from TimesPosts

Siyasa A Yau :::: BUƊAƊƊIYAR WASIKA ZUWA GA MAI GIRMA GWAMNAN JIHAR KANO, INJINIYA Abba Kabir Yusuf.
BUƊAƊƊIYAR WASIKA ZUWA GA MAI GIRMA GWAMNAN JIHAR KANO, INJINIYA Abba Kabir Yusuf.Take: Mulki amanar jama'a ne, amma mutunci da kyakkyawar mu'amala su ne ginshiƙin shugabanci.Mai girma Gwamna Abba…
Ay Abdullahi3 min read

Siyasa Nigeria A Yau ::: BABU MAI MURNA DA FARUWAR HAKA SAI MUTUMIN BANZA
BABU MAI MURNA DA FARUWAR HAKA SAI MUTUMIN BANZAAbinda yake faruwa a jihar Kano cibiyar Arewa bai yiwa duk wani mai mutunci dadi ba, babu mai murna da faruwar haka sai mutumin banzaAmma waye babban…
Ay Abdullahi2 min read

Siyasa Nigeria A Yau ::: Mai Yayi Zafi Haka kuwa
Matar Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, mai suna Zainab Musa Kwankwaso, ta shigar da ƙarar neman raba aurenta da gwamnan a wata kotun Upper Area Court da ke Gudu, a birnin Abuja, inda ta kuma…
Ay Abdullahi1 min read