Skip to content
TimesPosts homeTimesPostsThe record, as it happens.

Siyasa Nigeria A Yau ::: Komai yayi Zafi Haka kuma Ina makomar Siyasa Arewachin Nigeria A Yau

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi shugaban kwamitin yaƙi da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi na jihar, Barista Muhyi Magaji Rimin Gado, martani kan zargin cewa majalisar na jinkirta nazari kan kudirin…

Ay Abdullahi · Admin

· 1 min read

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi shugaban kwamitin yaƙi da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi na jihar, Barista Muhyi Magaji Rimin Gado, martani kan zargin cewa majalisar na jinkirta nazari kan kudirin dokar yaƙi da shaye-shaye da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya aika mata.

A cikin wata sanarwa da kakakin majalisar, Kamaluddeen Sani Shawai, ya fitar, majalisar ta ce ta karɓi kudirin kuma ta fara aiki a kansa, inda har aka yi karatun farko.

Sai dai majalisar ta ce gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2027 ne ya sa aka dakatar da ci gaba da nazarin kudirin, saboda kasafin kuɗi na da fifiko bisa tsarin gudanar da ayyukan gwamnati.

Ta kuma ce ba ta yi watsi da kudirin ba, kuma ba ta da wata manufa ta kawo masa cikas, tana mai jaddada goyon bayanta ga yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi da shaye-shaye.

Majalisar ta kuma shawarci Muhyi Magaji Rimin Gado da ya nemi ƙarin bayani kan yadda majalisa ke gudanar da ayyukanta kafin yin kalamai a bainar jama'a.

Me za ku ce?

More from TimesPosts