Skip to content
TimesPosts homeTimesPostsThe record, as it happens.

Siyasa Nigeria A Yau ::: Mai Yayi Zafi Haka kuwa

Matar Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, mai suna Zainab Musa Kwankwaso, ta shigar da ƙarar neman raba aurenta da gwamnan a wata kotun Upper Area Court da ke Gudu, a birnin Abuja, inda ta kuma…

Ay Abdullahi · Admin

· 1 min read

Matar Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, mai suna Zainab Musa Kwankwaso, ta shigar da ƙarar neman raba aurenta da gwamnan a wata kotun Upper Area Court da ke Gudu, a birnin Abuja, inda ta kuma bayyana aniyarta na ta mayar da sadakin aurensu.

Jaridar DAILY NIGERIAN ce ta rawaito hakan bisa wasu takardun kotu da ta samu, inda ta ce takardar gayyatar kotun mai lamba CV/97/26 ta umarci gwamnan da ya gurfana a gabanta ranar 17 ga watan Nuwamban shekarar 2026.

Zainab, wadda 'yar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ce, ta auri Abba Kabir Yusuf ne a ranar 29 ga watan Yulin shekarar 2006, lokacin yana hadimin mahaifinta, kuma yanzu haka suna da 'ya'ya shida. Ana zargin rikicin auren nasu dai ya faro ne sannu-sannu, kamar yadda majiyar jaridar ta shaida mata, da sai yanzu ne lamarin ya ta'azzara har ta kai ga kai ƙarar gwamnan kotu. Matar gwamna Abban dai na neman ya sake tan ne ta sigar Khulqi, wani tsarin saki da musulunci ya tanada bisa raɗin mata, da sharaɗin za ta mayar wa mijin sadakin da ya biya, idan kotu ta raba auren.

More from TimesPosts

Siyasa Nigeria A Yau ::: Mai Yayi Zafi Haka kuwa | TimesPosts