Siyasa Nigeria A Yau. :::: Mun biya Naira biliyan 37 na bashin ƴan fansho da mu ka gada - Gwamna Abba
Mun biya Naira biliyan 37 na bashin ƴan fansho da mu ka gada - Gwamna Abba Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ce gwamnatinsa ta biya Naira biliyan 37 daga cikin bashin fansho da giratuti da ta gada…
Ay Abdullahi · Admin
· 1 min read

Mun biya Naira biliyan 37 na bashin ƴan fansho da mu ka gada - Gwamna Abba
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ce gwamnatinsa ta biya Naira biliyan 37 daga cikin bashin fansho da giratuti da ta gada daga gwamnatocin baya.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin bikin sake biyan wasu tsofaffin ma’aikata da iyalan ma’aikatan gwamnati da suka rasu hakkokinsu a gidan gwamnatin Kano.
Ya ce gwamnatinsa ta fara sake biyan giratuti da alawus-alawus, inda wannan shi ne karo na bakwai da aka gudanar da irin wannan biyan kuɗi.
Abba Yusuf ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta kammala biyan sauran bashin da ake bin ta kafin watan Afrilun 2027.
Ya ce biyan kuɗaɗen na daga cikin ƙoƙarin gwamnatinsa na kula da jin daɗin ma’aikata, musamman waɗanda suka yi ritaya da iyalan waɗanda suka rasu.
A nasa ɓangaren, ƙungiyar tsofaffin ma’aikatan Najeriya (NUP) da ƙungiyoyin ƙwadago a jihar sun yaba wa gwamnatin bisa ba da fifiko ga walwalar ma’aikata da waɗanda suka yi ritaya.
Ƙungiyar NUP ta kuma karrama gwamnan da lambar yabo ta gwamnan da ya fi kula da ma’aikata, bisa ƙoƙarinsa na biyan haƙƙoƙin ma’aikata da iyalan waɗanda suka rasu.
More from TimesPosts

Siyasa Nigeria A Yau. ::: Matsin rayuwa da yan Nijeriya ke ciki zai iya baiwa APC matsala a Arewa a zaɓe mai zuwa - Kawu Sumaila
Matsin rayuwa da yan Nijeriya ke ciki zai iya baiwa APC matsala a Arewa a zaɓe mai zuwa - Kawu SumailaSanatan Kano ta Kudu, Suleiman Kawu, ya ce jam’iyyar APC na fuskantar ƙalubale wajen samun goyon…
Ay Abdullahi2 min read

Shin Maine Gaskiya Magana Akan Gwammana Abba Kabir Yusuf. :::: GWAMA ABBA BAI SAKI MATARSA BA
GWAMA ABBA BAI SAKI MATARSA BANa sa kudi Naira Miliyon uku (₦3,000,000) duk wanda ya kawo min hujja cewa Maigirma Gwamnan jihar Kano Engr Abba Kabir Yusuf ya saki matarsa Hajiya Zainab zan bashi…
Ay Abdullahi1 min read

Siyasa Nigeria A Yau. ::: Gwamna ba da matarsa yake ba
Gwamna ba da matarsa yake ba Musulunci bai yarda kotu ta sake bayanan ma’aurata ga yan jaridu ba. Aure babban al’amari ne; sirri ne tsakanin ma’aurata, hukumomi da Allah. Jaridar da ta sake labarin…
Ay Abdullahi2 min read