Siyasa Nigeria A Yau ::: Obi da magoya bayan NDC sun yi watsi da sabon taken Najeriya da Tinubu ya dawo da shi
Obi da magoya bayan NDC sun yi watsi da sabon taken Najeriya da Tinubu ya dawo da shi Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, tare da magoya bayan jam’iyyar, sun yi watsi da sabon…
Ay Abdullahi · Admin
· 1 min read

Obi da magoya bayan NDC sun yi watsi da sabon taken Najeriya da Tinubu ya dawo da shi
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, tare da magoya bayan jam’iyyar, sun yi watsi da sabon taken Najeriya, inda suka rera tsohon taken kasar yayin wani taron tattaunawa da jama’a a Legas.
Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis, lokacin da aka bukaci mahalarta taron su miƙe domin rera sabon taken Najeriya, amma Obi, dan takarar gwamnan Legas na NDC, Funso Doherty, da magoya bayansu suka ki.
Hakan ya sa mai gabatar da taron sauya taken zuwa tsohon inda mahalarta suka rera ta cikin farin ciki.
Obi ya kuma nuna goyon bayansa ga matakin, inda ya fuskanci taron tare da daga yatsu biyu a hannayensa biyu, a matsayin alamar tambarin jam’iyyar NDC.
Wannan na zuwa ne bayan wasu ’yan daba dauke da adduna, sanduna da duwatsu sun kutsa kai cikin wurin taron, lamarin da ya haddasa rudani tare da tilasta wa mahalarta taron tserewa domin tsira.
More from TimesPosts

Siyasa. INEC za ta yi biyayya ga hukuncin kotu kan cancantar Atiku a zaɓen 2027 – Amupitan
INEC za ta yi biyayya ga hukuncin kotu kan cancantar Atiku a zaɓen 2027 – AmupitanHukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta ce za ta yi biyayya ga duk wani hukuncin kotu kan cancantar tsohon…
Ay Abdullahi1 min read

Labaran Siyasa ::: Siyasa Nigeria ADC ba ta shiryawa zaɓen 2027 ba - Dalung
ADC ba ta shiryawa zaɓen 2027 ba - Dalung Tsohon ministan Matasa da Wasanni, Solomon Dalung, ya zargi Sakataren Jam’iyyar ADC na ƙasa, Rauf Aregbesola, da naɗa shugabannin kwamitocin riƙon ƙwarya a…
Ay Abdullahi1 min read

Labaran siyasa ::: Rikicin APC: Dan takara ya shigar da ƙara ga NEC da hukumomin tsaro
Rikicin APC: Dan takara ya shigar da ƙara ga NEC da hukumomin tsaroRikicin da ke cikin jam’iyyar APC a jihar Zamfara ya sake ɗaukar sabon salo, biyo bayan ƙorafin da wani dan takara Hassan Umar…
Ay Abdullahi1 min read