Siyasa Nigeria A Yau :::: Sanata Kawu Sumaila ya bai wa jami’an yaki da miyagun ƙwayoyi a Kano tallafin Naira miliyan 5
Sanata Kawu Sumaila ya bai wa jami’an yaki da miyagun ƙwayoyi a Kano tallafin Naira miliyan 5Sanatan Kano ta Kudu, Suleiman Abdulrahman Kawu Sumaila, ya yaba wa rundunar haɗin gwiwar hukumomi ta…
Ay Abdullahi · Admin
· 2 min read

Sanata Kawu Sumaila ya bai wa jami’an yaki da miyagun ƙwayoyi a Kano tallafin Naira miliyan 5
Sanatan Kano ta Kudu, Suleiman Abdulrahman Kawu Sumaila, ya yaba wa rundunar haɗin gwiwar hukumomi ta musamman da ke yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi a Kano, tare da ba jami’an rundunar tallafin Naira miliyan biyar.
Sanatan ya kuma bayar da gudummawar kayayyaki domin tallafa wa yaran da rundunar ta ceto daga mawuyacin hali, musamman wajen kula da su, kare su da kuma taimaka musu su samu ingantacciyar rayuwa.
Kawu Sumaila ya bayyana hakan ne yayin ziyarar da ya kai wa shugaban rundunar, Muhuyi Magaji Rimingado, ranar Laraba, 18 ga Nuwamba, 2026.
Ya ce ya yaba da jajircewa da sadaukarwar jami’an rundunar wajen yaƙi da matsalar shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da safararsu, yana mai cewa ayyukansu na taimakawa wajen kare al’umma da rage illolin da matsalar ke haifarwa.
Sanatan ya ce tallafin Naira miliyan biyar ɗin na da nufin ƙarfafa gwiwar jami’an da kuma nuna godiya bisa irin haɗarin da suke fuskanta wajen gudanar da aikinsu.
Dangane da yaran da aka ceto, Kawu Sumaila ya jaddada cewa cetonsu kaɗai bai isa ba, domin akwai buƙatar samar musu da kulawa, ilimi, kariya da damar samun makoma mai kyau.
Ya kuma yi kira da a ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin hukumomin gwamnati, sarakunan gargajiya, shugabannin al'umma, jami'an tsaro da ƙungiyoyin farar hula domin samun nasara a yaƙi da miyagun ƙwayoyi da matsalolin da suke haifarwa.
Da yake mayar da martani, shugaban rundunar, Muhuyi Magaji Rimingado, ya gode wa sanatan bisa tallafin kuɗi da kayan tallafi da kuma nuna damuwa kan halin da yaran da aka ceto suke ciki.
Ya bayyana tallafin Naira miliyan biyar a matsayin abin da zai ƙara wa jami’an rundunar ƙwarin gwiwar ci gaba da aikinsu.
Muhuyi ya sake jaddada aniyar rundunar na ƙara ƙaimi wajen yaƙi da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da fataucinsu, tare da inganta ayyukan jin ƙai da kare marasa galihu, musamman yara a faɗin Jihar Kano.
More from TimesPosts

Siyasa Nigeria A Yau ::: Komai yayi Zafi Haka kuma Ina makomar Siyasa Arewachin Nigeria A Yau
Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi shugaban kwamitin yaƙi da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi na jihar, Barista Muhyi Magaji Rimin Gado, martani kan zargin cewa majalisar na jinkirta nazari kan kudirin…
Ay Abdullahi1 min read

Siyasa Nigeria ::::: Tun farko Turai aka tura ni a matsayin jakadan Najeriya amma na nemi a dawo da ni Afrika ta Kudu - Fani-Kayode
Tun farko Turai aka tura ni a matsayin jakadan Najeriya amma na nemi a dawo da ni Afrika ta Kudu - Fani-Kayode Jakadan Najeriya a Afirka ta Kudu, Femi Fani-Kayode, ya bayyana cewa tun farko an tura…
Ay Abdullahi1 min read

Siyasa Nigeria A Yau. ::: Matsin rayuwa da yan Nijeriya ke ciki zai iya baiwa APC matsala a Arewa a zaɓe mai zuwa - Kawu Sumaila
Matsin rayuwa da yan Nijeriya ke ciki zai iya baiwa APC matsala a Arewa a zaɓe mai zuwa - Kawu SumailaSanatan Kano ta Kudu, Suleiman Kawu, ya ce jam’iyyar APC na fuskantar ƙalubale wajen samun goyon…
Ay Abdullahi2 min read