Siyasa Nigeria ::::: Tun farko Turai aka tura ni a matsayin jakadan Najeriya amma na nemi a dawo da ni Afrika ta Kudu - Fani-Kayode
Tun farko Turai aka tura ni a matsayin jakadan Najeriya amma na nemi a dawo da ni Afrika ta Kudu - Fani-Kayode Jakadan Najeriya a Afirka ta Kudu, Femi Fani-Kayode, ya bayyana cewa tun farko an tura…
Ay Abdullahi · Admin
· 1 min read

Tun farko Turai aka tura ni a matsayin jakadan Najeriya amma na nemi a dawo da ni Afrika ta Kudu - Fani-Kayode
Jakadan Najeriya a Afirka ta Kudu, Femi Fani-Kayode, ya bayyana cewa tun farko an tura shi aiki a wata ƙasa a Turai, amma ya nemi Shugaba Bola Tinubu da ya sauya masa wurin aiki zuwa Afirka ta Kudu.
Fani-Kayode ya bayyana hakan ne yayin liyafar cin abinci da ofishin jakadancin Najeriya da ke Pretoria suka shirya, bayan miƙa takardun shaidar fara aikinsa ga Shugaban Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, a ranar 13 ga Nuwamba, 2026.
Ya ce ya zaɓi Afirka ta Kudu ne saboda yana ganin Najeriya da ƙasar suna da rawar da za su taka wajen bunƙasa tattalin arziki da ci gaban yankin Afirka.
A cewarsa, ya nemi Shugaba Tinubu da ya tura shi Afirka ta Kudu maimakon ƙasar Turai da aka fara sanya shi, kuma shugaban ya amince da buƙatarsa.
Fani-Kayode ya ce Najeriya da Afirka ta Kudu ƙasashe ne masu tarihi da al'adu masu ƙarfi, don haka ya kamata su ƙarfafa alaƙarsu tare da guje wa duk wani abu da zai haddasa rashin fahimta ko rarrabuwar kai.
Tun da farko, an naɗa Fani-Kayode a matsayin jakadan Najeriya a Jamus, kafin daga bisani a sauya masa wurin aiki zuwa Afirka ta Kudu a watan Mayun 2026.
A wancan lokacin, tsohon ministan ya bayyana cewa ya gabatar da buƙata a hukumance ga tsohon Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Yusuf Tuggar, inda ya bayyana rashin jin daɗinsa da tura shi Jamus saboda wasu dalilai na kansa da kuma kasancewar ya shafe mafi yawan rayuwarsa a Turai.
Ya ce ya fi son zuwa Afirka ta Kudu, ƙasar da bai taɓa ziyarta ba, amma yake da matuƙar sha'awar saninta.
More from TimesPosts

Siyasa Nigeria A Yau :::: Sanata Kawu Sumaila ya bai wa jami’an yaki da miyagun ƙwayoyi a Kano tallafin Naira miliyan 5
Sanata Kawu Sumaila ya bai wa jami’an yaki da miyagun ƙwayoyi a Kano tallafin Naira miliyan 5Sanatan Kano ta Kudu, Suleiman Abdulrahman Kawu Sumaila, ya yaba wa rundunar haɗin gwiwar hukumomi ta…
Ay Abdullahi2 min read

Siyasa Nigeria A Yau ::: Komai yayi Zafi Haka kuma Ina makomar Siyasa Arewachin Nigeria A Yau
Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi shugaban kwamitin yaƙi da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi na jihar, Barista Muhyi Magaji Rimin Gado, martani kan zargin cewa majalisar na jinkirta nazari kan kudirin…
Ay Abdullahi1 min read

Siyasa Nigeria A Yau. ::: Matsin rayuwa da yan Nijeriya ke ciki zai iya baiwa APC matsala a Arewa a zaɓe mai zuwa - Kawu Sumaila
Matsin rayuwa da yan Nijeriya ke ciki zai iya baiwa APC matsala a Arewa a zaɓe mai zuwa - Kawu SumailaSanatan Kano ta Kudu, Suleiman Kawu, ya ce jam’iyyar APC na fuskantar ƙalubale wajen samun goyon…
Ay Abdullahi2 min read