Siyasa : Tsohon ministan wasanni da matasa, Solomon Dalung, ya yi ikirarin cewa magoya bayan jam’iyyar ADC sun samu kiran waya daga kabarin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari,
Tsohon ministan wasanni da matasa, Solomon Dalung, ya yi ikirarin cewa magoya bayan jam’iyyar ADC sun samu kiran waya daga kabarin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, inda aka umurce su da su zaɓi…
Ay Abdullahi · Admin
· 1 min read

Tsohon ministan wasanni da matasa, Solomon Dalung, ya yi ikirarin cewa magoya bayan jam’iyyar ADC sun samu kiran waya daga kabarin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, inda aka umurce su da su zaɓi Atiku Abubakar a zaɓen 2027.
Dalung, wanda jigo ne a ADC, ya bayyana hakan ne ranar Alhamis yayin wata hira da gidan talabijin na Channels TV a shirin Politics Today.
Ya ce Atiku, wanda shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, ya gaji tsarin siyasar tsoffin shugabannin ƙasa, Umaru Musa Yar’Adua da Muhammadu Buhari.
Ya kuma ce ziyarar da matar marigayi Buhari, Aisha Buhari, ta kai wa Atiku a gidansa da ke Abuja a watan da ya gabata, alama ce ta sauya goyon bayan siyasar Buhari zuwa ga Atiku.
“Saƙon da ta kai shi ne an yi nasarar sauya ƙuri’u miliyan 12 zuwa ga Atiku. Mun samu kiran waya daga kabarin Buhari cewa mu zaɓi Atiku,” in ji Dalung.
Ya bayyana cewa Buhari ya samu ƙuri’u miliyan 12.2 a zaɓen 2011, sannan miliyan 15.4 a 2015 da miliyan 15.2 a 2019.
Dalung ya nuna kwarin gwiwar cewa Atiku zai kayar da Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027, ko da kuwa APC ta yi ƙoƙarin hana ADC gudanar da yaƙin neman zaɓe.
Ya kuma ce goyon bayan da Atiku ke da shi a faɗin ƙasar ya fi taron jama’ar da wasu ’yan siyasa ke tarawa a lokacin gangamin yaƙin neman zaɓe, waɗanda ya kira “taron haya”.
Dalung ya taɓa riƙe muƙamin Ministan Wasanni da Matasa a gwamnatin Buhari daga Nuwamban 2015 zuwa Mayun 2019.
More from TimesPosts

Kasuwanchi. ::: Hadada Hannu Jari Dangote zai ƙara jari zuwa Dala biliyan 70 don bunƙasa kasuwancin sa a faɗin Afirka
Dangote zai ƙara jari zuwa Dala biliyan 70 don bunƙasa kasuwancin sa a faɗin AfirkaAttajirin ɗan kasuwa Aliko Dangote ya bayyana shirin ƙara zuba hannun jarin kamfaninsa a Afirka daga dala biliyan 50…
Ay Abdullahi1 min read

Siyasa Nigeria A Yau ::: Obi da magoya bayan NDC sun yi watsi da sabon taken Najeriya da Tinubu ya dawo da shi
Obi da magoya bayan NDC sun yi watsi da sabon taken Najeriya da Tinubu ya dawo da shi Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, tare da magoya bayan jam’iyyar, sun yi watsi da sabon…
Ay Abdullahi1 min read

Technology. ::: Ko Kunsan Mai yasa manta Shugaban Kasashe ke Rufe camera 📸 Idan Sunje Wajan Taro
Shin ko kasan dalilin da yasa manyan shugabannin ƙasashe suke sanya Tef ko Sticker a Camera 📸 ɗin wayoyin su a lokacin da suka halarci manyan taron ƙasashen duniya?. Malam this life is beyond your…
Ay Abdullahi2 min read