Tinubu ya amince cire tallafin mai ya jefa ’yan Najeriya cikin wahala
Tinubu ya amince cire tallafin mai ya jefa ’yan Najeriya cikin wahalaShugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince cewa cire tallafin man fetur ya jefa magidanta da dama a Najeriya cikin wahala, inda ya…
Ay Abdullahi · Admin
· 1 min read

Tinubu ya amince cire tallafin mai ya jefa ’yan Najeriya cikin wahala
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince cewa cire tallafin man fetur ya jefa magidanta da dama a Najeriya cikin wahala, inda ya ce gwamnatinsa na faɗaɗa hanyoyin sufuri masu rahusa domin rage wa jama’a raɗaɗin tsadar rayuwa.
Tinubu ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X ranar Lahadi, inda ya ce gwamnatin tarayya na haɗin gwiwa da gwamnatocin jihohi da masu zuba jari wajen samar da motocin bas, motocin lantarki da na iskar gas ta CNG.
Ya ce jihohin Ekiti sun samu motocin bas 15, Legas 20, yayin da Akwa Ibom ke da 50 da aka shirya fara aiki da su.
Haka kuma, Katsina ta samar da motocin bas 30 masu amfani da CNG da kekunan hawa na lantarki 200, yayin da Kano ta samu bas 30 masu amfani da CNG da wasu bas biyar masu amfani da lantarki.
Shugaban ya ƙara da cewa motocin bas 100 na CNG da ke jihar Kaduna sun yi jigilar fasinjoji sama da miliyan uku.
Tinubu ya ce cibiyoyi sama da 400 da gwamnati ta amince da su sun mayar da motoci sama da 120,000 zuwa masu amfani da CNG, tare da ƙara faɗaɗa wuraren samun iskar domin rage kuɗin sufuri.
Ya kuma bayyana cewa gwamnati ta yi rangwame kan harajin mai da wasu kuɗaɗen da suka haura naira tiriliyan 3.3 domin rage tasirin tsadar mai ga jama’a da ’yan kasuwa.
A cewarsa, kamfanin NNPC zai dakatar da karɓar ribarsa na tsawon kwanaki 30, tare da ba masu harkar sufuri na jama’a fifiko. Ya kuma ce gwamnati na ƙoƙarin takaita kuɗin da ake sayar da man fetur ga ’yan kasuwa a matakin jumulla zuwa naira 1,350 kan kowace lita, domin rage sauyin farashi.
More from TimesPosts

DA DUMI-DUMI: Gwamnatin tarayya ta sanar da rage farashin man fetur
DA DUMI-DUMI: Gwamnatin tarayya ta sanar da rage farashin man fetur Gwamnatin tarayya ta sanar da shirin rage farashin man fetur da ake sayarwa a gidajen mai na Kamfanin mai na kasa (NNPC) na tsawon…
Ay Abdullahi1 min read

Siyasa Duniya A Yau Ko Kunsan Da Gabas Ta Tsakiya ke chiki
Da Dumi-Duminsa:Iran za ta ƙara nisan zangon makamanta masu linzami Zuwa Kilomita 1000 bayan Sojin Amurka Sun Sake Sansani a Tekun IndiaWani kakakin sojojin Iran, Mohammad Akraminia, ya bayyana cewa…
Ay Abdullahi1 min read

Siyasa Arewachin Nigeria Shin Haka Da gaskene
Matsaloli Goma da Suke Gaban Abba Kabir Yusuf a Zaben 2027.1. Karfin Kwankwasiyya da Kwankwaso2. Rashin sakin jiki da yan tsohuwar APC.3. Masu yiwa Kwankwasiyya aiki acikin gwamantin shi.4. Rashin…
Ay Abdullahi1 min read