Skip to content
TimesPosts homeTimesPostsThe record, as it happens.

Wani masanin fasaha daga Iran, Hamid Naderi Yeganeh, wanda yake amfani da lissafi na lambobi wajen ƙirƙirar zanen hotuna masu ban mamaki.

Wani masanin fasaha daga Iran, Hamid Naderi Yeganeh, wanda yake amfani da lissafi na lambobi wajen ƙirƙirar zanen hotuna masu ban mamaki.Ba ya zana su kamar yadda mai zane yake yi.Yana amfani da…

Ay Abdullahi · Admin

· 1 min read

Wani masanin fasaha daga Iran, Hamid Naderi Yeganeh, wanda yake amfani da lissafi na lambobi wajen ƙirƙirar zanen hotuna masu ban mamaki.

Ba ya zana su kamar yadda mai zane yake yi.

Yana amfani da ƙa’idojin lissafi (mathematical equations) wajen samar da dubban layuka da siffofi. Daga nan sai ya gyara su a hankali, har su zama hoton da kake iya gani.

Abin mamaki shi ne... Daga lambobi da ƙa’idojin lissafi… sai ka ga irin wannan tsari mai kyau ya fita kamar na jikin hoton nan.

To ka ɗan tsaya ka yi tunani.

Idan lissafi zai iya samar da irin wannan tsari mai ban mamaki…

Ta yaya ma za mu iya tabbatar da cewa duniyar da muke ciki ba wani babban tsarin lissafi ba ne wanda muka kasa fahimta?

Wataƙila ba za mu iya amsa wannan tambayar ba.

Amma tambayar kanta ta isa ta sa mutum ya kalli duniyar da wani sabon idanun.

#DigitalPsychologist @topfans

More from TimesPosts