Skip to content
TimesPosts homeTimesPostsThe record, as it happens.

Wannan hoton plain radiographic scan ne na jiki, ku kalli tarin ƙibar ta gefe da gefe, sannan daga tsakiya kuma kalli ƙashinta ka gani. Huhun a takure yake, sannan kashin gadon bayar

Wannan hoton plain radiographic scan ne na jiki, ku kalli tarin ƙibar ta gefe da gefe, sannan daga tsakiya kuma kalli ƙashinta ka gani. Huhun a takure yake, sannan kashin gadon bayar ya zaizaye…

Ay Abdullahi · Admin

· 2 min read

Wannan hoton plain radiographic scan ne na jiki, ku kalli tarin ƙibar ta gefe da gefe, sannan daga tsakiya kuma kalli ƙashinta ka gani. Huhun a takure yake, sannan kashin gadon bayar ya zaizaye dalilin daukar nauyi.

Wannan tarin tsokar da kitse akan ƙashi na da matukar illa sosai, shi yasa nake mamaki da aka ce cikin Mata da Maza wasu har magunguna da supplements suke sha domin sui ƙiba, sui teɓa.

..................................................................

Tarin kitse da tsoka na ƙara nauyi da matsi ga ƙasusuwa tare da kayan ciki, amma babu kamar ƙasusuwa wato bones domin duk wannan nauyin ƙashi ne ke ɗaukesa, wanda in muka kalli abin da kyau ba ƙaramin lodi bane akan ƙasusuwa musamman na guiwa, ƙugu, da gadon baya.

Wannan matsi na lodin nauyin tsoka da kitse na iya haifar da:

1. Cinyewar guiwoyi da gurun-guntsi wanda ke haddasa zafi, zogi da sanadarewar guiwoyi (osteoarthritis)

2. Raguwar ƙarfi da ƙarko na ƙashi ta yadda yakan zagwanye

3. Saurin tsagewa, targaɗe ko karyewar ƙashi haka kurum ko in an sami ƙaramar faɗuwa.

Tarin tsoka dede da jiki wato kakkauran mutum wannan ba matsala bane, domin madaidaiciyar tsokar na taimakawa ƙashi ya zama mai ƙarfi saboda motsa jiki yana ƙara yawan ƙwayoyin ƙashi da ƙarfin tsayuwa.

Amma idan tsokar ta yi yawa batare da daidaito ba (musamman tare da ƙiba), tana ƙara nauyi da matsin ƙarin lodi kan guiwoyi (joints).

..................................................................

Sannan ta daya ɓangaren Ƙiba na daga alamun yawan kitse a jiki fiye da ƙima wanda zuwa gaba can na iya jawo matsaloli da dama ga lafiyar jiki, kamar:

• Hawan jini da ciwon zuciya

• Ciwon sugar (diabetes nau’i na 2)

• Ciwon guiwoyi da baya

• Matsalar minshari da ɗaukewar numfashi yayin bacci (sleep apnea)

• Ciwon hanta da ciwon ƙoda

• Da kuma ƙara hatsarin kamuwa da wasu cututtuka kamar cancers, numoniya da sauransu.

A takaice, ƙiba da tarin kitse suna ƙara nauyin da ƙashi ke ɗauka, suna haifar da matsalolin gwiwoyi da ciwon ƙashi.

Motsa jiki tare da cin abinci me kyau dede gwargwado na taimakawa wajen kiyaye nauyi, ƙarfi da lafiyar ƙashi.

Bazaki iya rage nauyi ba idan baki dena ciye-ciyen abubuwan da kike ba, ba wai zama aci abinci ba, a'a wannan abubuwan kwadayin ci biscuit, ci chocolates, ci gireba da sauransu su zasu saki ƙiba.

Kuma duk wanda yace Exercise baya sashi rage nauyi....toh ka sani ba da gaske yake ba.

More from TimesPosts