Za mu dawo da tallafin man fetur - Kwankwaso
Za mu dawo da tallafin man fetur - Kwankwaso Mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce jam’iyyar za ta ɗauki duk matakan da suka dace, ciki har da dawo da…
Ay Abdullahi · Admin
· 1 min read

Za mu dawo da tallafin man fetur - Kwankwaso
Mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce jam’iyyar za ta ɗauki duk matakan da suka dace, ciki har da dawo da tallafin man fetur, domin rage farashinsa idan ta lashe zaɓen 2027.
Kwankwaso, tsohon gwamnan Kano, ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Channels TV a shirin Politics Today ranar Alhamis.
Ya ce har yanzu ’yan Najeriya ba su farfaɗo daga girgizar tattalin arzikin da cire tallafin man fetur ya haifar ba tun bayan da Shugaba Bola Tinubu ya sanar da matakin a ranar 29 ga Mayun 2023.
A cewarsa, farashin makamashi a ƙasar ya yi tsada matuƙa, lamarin da ke ƙara jefa jama’a cikin wahalhalun rayuwa.
Kwankwaso ya bayyana cewa NDC ta tattauna kan hanyoyin magance matsalar, yana mai cewa ya kamata a yaƙi cin hanci da rashawa a masana’antar man fetur domin sauƙaƙa wa ’yan Najeriya.
Ya ce matsayar jam’iyyar ita ce za ta yi duk abin da ya dace, har da yiwuwar dawo da tallafin, domin rage farashin man fetur da sauƙaƙa rayuwar talakawa.
A watan Satumban 2026, ɗan takarar shugaban ƙasa na NDC, Peter Obi, ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta iya dawo da tallafin man fetur bayan ta magance matsalar cin hanci da rashawa.
Haka kuma, tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, wanda ke takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar ADC, ya ce zai dawo da tallafin idan ya lashe zaɓen 2027.
Ɗan takarar jam’iyyar PRP, Donald Duke, shi ma ya yi alƙawarin rage farashin litar man fetur zuwa kusan naira 300 idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa.
More from TimesPosts

WAI SHIN MAINE GASKIYA WANNA MAGANA : El-Rufai Yayi Yunkurin Bawa Jamian EFCC Cin Hancin Dala Dubu Dari Shida - a Cewar Shedan SSS a Kotu
El-Rufai Yayi Yunkurin Bawa Jamian EFCC Cin Hancin Dala Dubu Dari Shida - a Cewar Shedan SSS a KotuWani mai binciken laifuka na hukumar tsaro ta farin kaya (SSS) ya bayyana a gaban kotu cewa tsohon…
Ay Abdullahi1 min read

Gwamnatin tarayya ta tsara ware Naira biliyan 84.48 domin aiwatar da shirin kawo ƙarshen auren ƙananan yara a Najeriya nan da shekarar 2030.
Gwamnatin tarayya ta tsara ware Naira biliyan 84.48 domin aiwatar da shirin kawo ƙarshen auren ƙananan yara a Najeriya nan da shekarar 2030.Ministar harkokin mata da ci gaban al’umma, Imaan…
Ay Abdullahi1 min read

Tinubu ya amince cire tallafin mai ya jefa ’yan Najeriya cikin wahala
Tinubu ya amince cire tallafin mai ya jefa ’yan Najeriya cikin wahalaShugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince cewa cire tallafin man fetur ya jefa magidanta da dama a Najeriya cikin wahala, inda ya…
Ay Abdullahi1 min read