Amurka Ba Akan Tsarin Dimokuraɗiyya Ta Samu Power Ba.
Amurka Ba Akan Tsarin Dimokuraɗiyya Ta Samu Power Ba.A shekarun 1950s, Koriya ta Kudu tana daga cikin ƙasashe mafi talauci a duniya. Amma daga baya ta samu wani gagarumin sauyi, ta koma ƙasa mai…
Ay Abdullahi · Admin
· 4 min read

Amurka Ba Akan Tsarin Dimokuraɗiyya Ta Samu Power Ba.
A shekarun 1950s, Koriya ta Kudu tana daga cikin ƙasashe mafi talauci a duniya. Amma daga baya ta samu wani gagarumin sauyi, ta koma ƙasa mai ƙarfin arziki da masana'antu, fasaha da tattalin arziki.
Bankin Duniya ya bayyana wannan a matsayin ɗaya daga cikin manyan sauye-sauyen ci gaba da aka samu a zamaninmu, wanda ya haɗa da saka jari a fannin ilimi, ababen more rayuwa, fasaha da ingantaccen tsarin tattalin arziki.
China ma ta ba duniya wani babban mamaki. Tun bayan sauye-sauyen tattalin arziki da suka fara a shekarar 1978, tattalin arzikin China ya girma da matsakaicin percent fiye da kashi 9 cikin 100 a shekara, kuma kusan mutane miliyan 800 sun fita daga cikin matsanancin talauci.
Wannan ba yana nufin tsarin China shi ne tsarin da kowace ƙasa ya kamata ta kwaikwaya ba. Darasin shi ne ci gaban ƙasa yana da abubuwa da yawa fiye da tsarin democracy kadai.
Ga tambaya.... Idan dimokuraɗiyya ita ce mabuɗin ci gaban ƙasa, me ya sa wasu ƙasashen suka samu gagarumin sauyin tattalin arziki da cigaba kafin su koma cikakken tsarin dimokuraɗiyya?
Amurka ma ta gina ƙarfinta ne tun a cikin zamanin bautar da mutane ba da tsarin dimokuraɗiyya ba.
Akwai wani masani ɗan Koriya ta Kudu mai suna Ha-Joon Chang wanda ya yi wani muhimmin bincike a kan tarihin ci gaban ƙasashe masu arziki.
A cikin littafinsa na Kicking Away the Ladder (wato wanda ya hau sama ya ture tsani), ya yi tambaya mai sauƙi amma mai nauyi da take da wuyar amsa cewa... Ta yaya ƙasashen da suka zama masu arziki a yau suka samu nasu arzikin, tun kafin su fara ba sauran ƙasashe shawarar yadda za su samu ci gaba?
Bincikensa ya nuna cewa ƙasashe da dama da suke ci gaba a yau sun yi amfani da masana'antu, haraji kan kayayyakin da ake shigo dasu daga waje, tallafin gwamnati da wasu manufofin kare masana'antunsu, yayin da suke ƙoƙarin kamowa kasashen da suka riga su ci gaba.
Shin ƙasashe masu tasowa kamar Nigeria ko Niger suna da damar gina tsarin tattalin arzikinsu daidai da yanayinsu, ko kuwa dole sai sunbi tsari irin na kasashen da sun dade da samun cigaba?
Idan muka koma tarihin Afirka bayan samun 'yancin kai, za mu ga cewa siyasar duniya, Yaƙin Cacar Baki, albarkatun ƙasa da muradun ƙasashen waje sun taka rawa a wasu muhimman abubuwan da suka faru damu a yanzu. Misali, batun Patrice Lumumba na Congo ba ƙaramin tarihi ba ne.
Takardun da aka saki daga baya sun nuna cewa CIA ta shiga shirye-shiryen cire Lumumba daga mulki, har ma aka tsara wata hanya ta kashe shi. Amma tarihin mutuwarsa ya fi wannan rikitarwa. Belgium da wasu 'yan siyasar Congo da sauran ɓangarori ma sun taka muhimmiyar rawa.
A tarihin Afirka, ba za mu iya fahimtar matsalolin siyasa da tattalin arziki ta hanyar kallon abin da ke faruwa a cikin ƙasa daya kawai ba.
Akwai kuma batun Kwame Nkrumah na Ghana.
Nkrumah yana ƙoƙarin gina Ghana mai zaman kanta ta fuskar tattalin arziki da siyasa, amma dangantakarsa da ƙasashen Yamma ta yi tsami sosai. A shekarar 1966, sojoji da 'yan sanda suka kifar da gwamnatinsa yayin da yake tafiya zuwa Beijing.
Takardun gwamnatin Amurka sun nuna cewa Amurka ta san da shirye-shiryen juyin mulkin, amma bayanan da aka bayyana ba su tabbatar da cewa gwamnatin Amurka ce ta shirya juyin mulkin ba.
Wannan bambancin yana da muhimmanci.
Domin idan muna son fahimtar tarihi da gaske, bai kamata mu mayar da kowanne abu zuwa yammacin duniya ne ya yi komai ko kuma Afirka ce kawai ke da laifi ba.
Akwai kuskuren shugabannin Afirka. Akwai cin hanci da rashawa. Akwai raunin hukumomi. Akwai rikice-rikicen kabilanci da siyasa.
Amma akwai kuma tarihin mulkin mallaka, tasirin manyan ƙasashe, yaƙe-yaƙen siyasa, kasuwancin albarkatun ƙasa, bashi da dangantakar tattalin arziki tsakanin ƙasashe masu ƙarfi da masu tasowa.
Rashin cigaban Africa... Ba dimokuraɗiyya kaɗai ba ce. Ba mulkin kama-karya kaɗai ba ne. Ba albarkatun ƙasa kaɗai ba ne. Ba Turawa kaɗai ba ne. Ba shugabannin Afirka kaɗai ba ne. Matsalar ta fi haka zurfi.
Kuma watakila babban darasin da Afirka za ta koya daga tarihin duniya shi ne cewa ƙasa ba ta samun ci gaba saboda tsarin dimokuraɗiyya kawai, tana samun ci gaba ne idan ta iya gina ilimi, masana'antu, ayyukan yi, ingantattun hukumomi, fasaha da tattalin arzikin da ke amfani da albarkatunta domin amfanin jama'arta.
Idan Najeriya da sauran ƙasashen Afirka suna da matasa, albarkatun ƙasa da manyan kasuwanni, me ya hana mu gina irin wannan ƙarfin?
#DigitalPsychologist @topfans
More from TimesPosts

JAPANESE COMPANIES ARE LEAVING CHINA IN RECORD NUMBERS
JAPANESE COMPANIES ARE LEAVING CHINA IN RECORD NUMBERSThe number of Japanese companies operating in China down 22% since 2024 to its lowest level since Teikoku Databank started tracking in 2010.4,137…
Ay Abdullahi1 min read

Siyasa Duniya A Yau. MUMMUNAR ZANGA-ZANGAR TA RINCABE A P@KISTAN
MUMMUNAR ZANGA-ZANGAR TA RINCABE A P@KISTAN Yanzu haka magoya bayan wannan mashahuran mutumin na P@kistan IMRAN Kh@n sun fara zanga-zangar dole a sake shi .Imran Khan shi ne tsohon Firayim Ministan…
Ay Abdullahi1 min read

White House news
“I am announcing the formation of the Super Intelligence Force (SIF). The Super Intelligence Force is tasked with coordinating the effort of the Federal Government to ensure that America continues to…
Ay Abdullahi1 min read