BUƊAƊƊIYAR WASIƘA ZUWA GA MAIGIRMA GWAMNAN JIHAR KANO ENGINEER ABBA KABIR YUSUF!
BUƊAƊƊIYAR WASIƘA ZUWA GA MAIGIRMA GWAMNAN JIHAR KANO ENGINEER ABBA KABIR YUSUF!Da sunan Allah mai rahama mai Jin ƙai, Allah ya yi daɗin tsira ga shubanmu Annabi Muhammad (SAW)Bayan gaisuwa tare da…
Ay Abdullahi · Admin
· 4 min read

BUƊAƊƊIYAR WASIƘA ZUWA GA MAIGIRMA GWAMNAN JIHAR KANO ENGINEER ABBA KABIR YUSUF!
Da sunan Allah mai rahama mai Jin ƙai, Allah ya yi daɗin tsira ga shubanmu Annabi Muhammad (SAW)
Bayan gaisuwa tare da fatan alheri gareka ya maigirma gwamna, na garzayo ne a guje domin neman alfarma a wajenka.
Ina rubuta wannan buɗaddiyar wasiƙar ne da nufin janyo hankalinka ga wani al'amari mai matuƙar tayar da hankali da ke faruwa a jiharmu ta Kano mai albarka da kake jagoranta. A halin yanzu, ana tsare da wani matashin ɗalibi a gidan yari wanda ake kira Aiha K/Nasarawa wanda nake tunanin ya yi wani ƙaramin laifi (minor offence) wanda ya faru sanadiyyar ra'ayi na siyasa. Wannan mataki ba wai kawai yana lalata makomar wannan matashi ba ne, har ma yana sa ya rasa darussa (classes) da kuma jarrabawar gwaji a makaranta.
Maigirma Gwamna, babban aikin gidan yari a tsarin mulki na zamani shi ne gyaran hali (rehabilitation), ba wai zama makami na hukunci ko murƙushe ra'ayin matasa ba. A daidai lokacin da Majalisar Ɗinkin Duniya (UNODC) take kira da a rage cinkoso a gidajen yari saboda tsananin bazuwar cututtuka da kuma matsalar tattalin arziki, bai dace mu riƙa amfani da gidajen yari don ajiye matasanmu da suke da gurbi a jami’o’i ko kasuwanni ba, matuƙar laifinsu ba na zubda jini ba ne ko kuma munanan aiyuka ba.
Gwamna, a fadin duniya, ƙasashen da suka ci gaba suna fafutuka da fuskantar sauye-sauye na gyaran tsarin gidajen yari (prison reforms). A ƙarƙashin waɗannan tsarukan sauye-sauye, babban burinsu shi ne a horar da mutane da kuma taimakawa masu laifi ko waɗanda suka taɓa yin laifi (offenders and previous offenders) hanyoyin da za su kiyaye kansu daga sake aikata abubuwan da za su kai su gidan yari. Muna sane kuma muna yaba wa ƙoƙarin gwamnatinka wajen ƙaddamar da yaƙi da shaye-shaye a tsakanin matasa; wannan babban mataki ne na kiyaye afkuwar laifuka. Don haka, muna kira da ka yi koyi da tsarin ƙasashen duniya ta hanyar amfani da dabarun gyaran hali maimakon tsauraran hukunce-hukuncen garkame matasa ‘yan adawa.
Bugu da ƙari, ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta duniya, ‘Amnesty International’ ta bayyana, akwai buƙatar a saki wannan matashi da ma sauran matasan da aka garƙame. Domin shugabanni kun yi alƙawarin kare haƙƙin ɗan adam, lallai ya kamata a ba wa 'yan adawa da matasa damarsu ta fadin albarkacin baki (freedom of expression) kamar yadda tsarin mulki ya tanada. Inda matasa suka kuskure a duba yiwuwar yi musu hukuncin su koma su ƙaryata kansu ko kuma a hanasu gudanar da shafukansu na tsawon wani lokaci.
Ban san ɗalibin nan ba sai a nan social media kuma bani da wata alaƙa da shi ko ta kusa ko ta nesa, sai ta kasancewarmu jiha ɗaya amma lallai na tausaya masa a matsayinsa na ɗalibi ya rasa wasu ajujuwa na karatunsa, na tabbata wannan abin zai kawo masa tawaya mai girma a karatunsa.
Ina rokonka akan kasa baki a saki wannan ɗalibin na sashen aikin shari’a Aiha K/Nassarawa da ke garƙame a gidan gyaran hali.
Ya maigirma gwamna lallai na kusa shekara rabona da social media saboda duƙufa a faggen karatu sai dai ganin labarin wannan ɗalibi ya shahara a ‘international forum’ har ya zama ana ganin gwamnatinka ta tsaurara hukunci shi ya sa na garzayo da ƙoƙon bara.
A shawarce maimakon gidan yari, irin waɗannan ƙananan matsaloli ana magance su ne ta hanyar gargaɗi ko hidimar al'umma (community service).
Ya Maigirma gwamna ina kira gare ka da ka yi amfani da ikonka na uba kuma shugaba ka sa baki:
1. A saki wannan ɗalibi cikin gaggawa domin ya koma aji ya ci gaba da karatunsa.
2. A tabbatar an mutunta haƙƙin 'yan adawa na bayyana ra'ayoyinsu cikin lumana ba tare da fargabar tsarewa ba.
Ina fatan za ka duba wannan buƙata da idon rahama da hangen nesa na shugabanci na gari.
Ina Godiya da girmamawa, tare da saka ran cewa za ka karɓi shawarata.
Sa’adatu Baba Ahmad ɗaliba ce mai karatun digiri na uku ‘PhD’a sashen ‘Media and International Journalism’ a jami’ar Bedfordshire da ke nan Ingila, ina yin bincike Akan ‘AUNA TASIRIN FAFUTUKAR DA KAFOFIN YAƊA LABARAI KE JAGORANTA WAJEN FAƊAƊA TSARIN MANUFOFI DA GYARAN SHUGABANCI A NAJERIYA: TARE DA NAZARI AKAN DOKAR MASANA'ANTAR MAN FETUR (PIA) DA RAWAR DA TAKE TAKAWA WAJEN RAGE SAUYIN YANAYI.
Source Daily Nigeria hausa
saababaahmad@yahoo.com
sa’adatubabaAhmad@study.beds.ac.uk
More from TimesPosts

Shin Ko maine Dalili ... ?
A karo na 2 Najeriya ta yi bikin ’yancin kai ba tare da faretin sojoji baGwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta gudanar da bikin cikar Najeriya shekaru 66 da samun ’yancin kai ba tare da faretin…
Ay Abdullahi1 min read

Wasu Muhimman Batutuwa Da Mai Girma Shugaban Kasar Nigeria Yayi A Ranar Da Kasar Tasamu Yanchi Dr Ahmad Bola Tinubu
Muhimman abubuwa 10 da ke cikin jawabin Tinubu na ranar ƴancin kai1. Tattalin arziki ya fara samun ci gaba: Ya ce tattalin arzikin Najeriya ya samu bunƙasa da sama da kashi 4% a shekarar 2026.2.…
Ay Abdullahi1 min read

Shin Ko Haka Zatayi Kuwa..?
Shugabannin wasu jam’iyyun adawa a Najeriya sun ƙara kaimi wajen tattaunawa kan samar da ɗan takarar shugaban ƙasa guda ɗaya da zai wakilci ɓangaren adawa a zaɓen 2027.A wani sabon mataki na…
Ay Abdullahi1 min read