HAƊARIN YIN JIMA'I DA MACEN DA BA KA SANI BA
HAƊARIN YIN JIMA'I DA MACEN DA BA KA SANI BA…Kada kayi gaggawar yin jima'i da macen da baka sani ba kawai saboda sha'awa tana jagorantar ka.Wani lokaci, sha'awa ta ɗan lokaci tana iya jefa mutum…
Ay Abdullahi · Admin
· 1 min read

HAƊARIN YIN JIMA'I DA MACEN DA BA KA SANI BA…
Kada kayi gaggawar yin jima'i da macen da baka sani ba kawai saboda sha'awa tana jagorantar ka.
Wani lokaci, sha'awa ta ɗan lokaci tana iya jefa mutum cikin matsalolin da zai daɗe yana nadama, ba ta fuskar jikinka kaɗai ba, har ma da zuciya da kuma ruhi (Spirituality).
Yin jima'i da macen da ba ka sani ba na iya jefa ka cikin haɗarin kamuwa da cututtukan da ake ɗauka ta hanyar jima'i (STIs), ciki marar shiri, damuwa ta zuciya, da kuma matsalolin da ka iya tasowa sakamakon rashin fahimtar junanku.
Ta fuskar ilimin metaphysics, wasu koyarwar suna kallon kusancin jima'i a matsayin wani abu da ya wuce iya haɗuwar jiki kawai. Suna danganta shi da kusancin zuciya, motsin rai da kuma yadda mutum yake jin kansa bayan anyi wannan hulɗa.
Macen da take da Law vibrational energy ko namiji yana iya janki cikin wannan kaddarar tasa mummuna spiritually kuma ki kasa gano mene ne matsalar.
Wannan yana da alaƙa da yadda masu yin haka ke shiga wani irin hali maza da matan koda kuwa sunyi arziki dashi, kana iya samunsu da rashin nutsuwar jiki da kuma samun cikar muradun rayuwa.
Idan ka saba bin kowace sha'awa ba tare da kamun kai ba, hakan na iya shafar yadda kake yanke shawara da kuma yadda kake gudanar da rayuwarka.
Ba kowace sha'awa ce ya kamata ka bi ba. Wani lokaci, ikon da ka ke dashi akanka na cewa A'a shi ne zai kare ka da lafiyarka, mutuncinka da kwanciyar hankalinka.
Kada ka bari jin daɗin ɗan lokaci ya sa ka manta da lafiyarka, imaninka da makomarka.
Ka mallaki sha'awarka, zakayi abinda mutane dayawa ba za su iya ba a rayuwa.
#DigitalPsychologist @topfans
More from TimesPosts

S+xually transmitted diarrhea is on the rise and becoming difficult to treat — Report
S+xually transmitted diarrhea is on the rise and becoming difficult to treat — Report Shigella, a bacterial infection that causes dysentery, is increasingly spreading through s+xual contact, while…
Ay Abdullahi2 min read

SABBIN IYAYE KU KOYI HAƘURI
SABBIN IYAYE KU KOYI HAƘURI Haihuwa ɗaukaka ce, bakuwa a samun daukaka sai anjure, iyayen mu nada shiri suke mata na gaske, shiyasa wata saita gama naƙuda ta haihu ɗaki daya ga mijinta yana Bacci…
Ay Abdullahi3 min read

Jinin Al’ada Na Iya Zama Wani Abu Mai Muhimmanci Ga Magunguna Anan Gaba
Jinin Al’ada Na Iya Zama Wani Abu Mai Muhimmanci Ga Magunguna Anan Gaba.Abin da mata da yawa suke zubarwa duk wata, masana kimiyya sun gano cewa yana ɗauke da wasu ƙwayoyin da za su iya taimakawa…
Ay Abdullahi1 min read