Skip to content
TimesPosts homeTimesPostsThe record, as it happens.

SIHIRIN SAKAWA MACE ZUBAR JINI

SIHIRIN SAKAWA MACE ZUBAR JINI WATO SIHRUN NAZIYF (سحر النزيف) Acikin Littafin Sunan Abī Dāwūd, hadisi na 287 da Jāmi‘ut-Tirmidhī, hadisi na 128 da Sunan Ibn Mājah, hadisi na 627, an ruwaito hadisi…

Ay Abdullahi · Admin

· 6 min read

SIHIRIN SAKAWA MACE ZUBAR JINI

WATO SIHRUN NAZIYF (سحر النزيف)

Acikin Littafin Sunan Abī Dāwūd, hadisi na 287 da Jāmi‘ut-Tirmidhī, hadisi na 128 da Sunan Ibn Mājah, hadisi na 627, an ruwaito hadisi mai tsawo wanda Sheikh Nasirud Dinil Albaniya ya inganta shi cewa:

An karɓo daga Hamnah 'yar Jahsh رضي الله عنها, ta ce:

“Na kasance ina fama da zubar jini mai yawa da tsanani. Sai na je wurin Annabi ﷺ domin neman fatawa da bayyana masa halin da nake ciki. Na same shi a gidan 'yar uwata Zainab bint Jahsh.

Sai na ce: Ya Manzon Allah, ina fama da zubar jini mai yawa da tsanani. Me kake gani game da wannan halin? Domin ya hana ni yin sallah da azumi.

Sai ya ce: ‘Zan ba ki shawarar amfani da auduga, domin tana taimakawa wajen tsayar da jini.’

Ta ce: ‘Jinin ya fi haka yawa.’

Ya ce: ‘To, ki ɗaure wani kyalle domin riƙe jinin.’

Ta ce: ‘Jinin ya fi haka yawa; yana zuba sosai.’

Sai ya ce: ‘Zan umarce ki da abubuwa biyu; duk wanda kika aikata daga cikinsu zai wadatar da ke daga ɗayan. Idan kuma za ki iya yin su duka, to ke kika fi sanin yanayinki. Wannan bugun Shaiɗan ne. Ki ɗauki kwanaki shida ko bakwai a matsayin kwanakin hailarki......"

Izuwa ƙarshen Hadisin..

Imam Al-Khaṭṭābī (الخطابي)

A cikin littafinsa معالم السنن ya bayyana ma'anar wannan lafazi da cewa

«مَعْنَاهُ أَنَّ الشَّيْطَانَ قَدْ وَجَدَ بِذَلِكَ طَرِيقًا إِلَى التَّلْبِيسِ عَلَيْهَا فِي أَمْرِ دِينِهَا، وَوَقْتِ طُهْرِهَا وَصَلَاتِهَا، حَتَّى أَنْسَاهَا ذَلِكَ، فَصَارَ فِي التَّقْدِيرِ كَأَنَّهُ رَكْضَةٌ نَالَتْهَا مِنْ رَكْضَاتِهِ».

Ma'ana:

“ Wannan Hadisi ma'anarsa ita ce Shaiɗan ya samu hanyar rikita mata al'amuran addininta, musamman game da lokacin tsarkinta da sallarta, har hakan ya jawo mata ruɗani. Saboda haka, a wajen misali, ya zama kamar wani bugun da ta samu daga cikin bugun Shaiɗan.”

Wannan na nuna cewa Shaiɗan na iya shafar ko haɗa alaƙa da zuwan jinin mace domin saka mata ruɗi sa wasuwasi, koda dai hadisin bai ambaci cewa asiri aka yi ma ta ba amma ya tabbatar da cewa daga Shaiɗan ne.

Shaikh Waheed bin Abdus-Salam Bali ya kawo bayani a kan wannan nau'in sihiri a cikin littafinsa

«الصارم البتار في التصدي للسحرة الأشرار»،

inda ya yi amfani da sunan سحر النزيف (Sihrun Nazīf), tare da fassara shi da cewa shi ne zuwan jinin الاستحاضة (Istihāḍah), wato zubar jinin mace ba a lokacin al'adarta ta ba.

Haka nan Shaikh Khalid bin Abdur-Rahman Al-Juraishi ya ambaci wannan nau'in a cikin littafinsa «الحذر من السحر»، inda ya yi amfani da sunan سحر النزيف.

Malaman ruƙiyyah sun fassara Sihrun Naziyf da cewa 'Shi ne sihirin da ake yi domin sabbabawa macewa zubar jini daga cikin mahaifarta ba bisa ƙa'ida ba kuma ba lokacin zuwan jinin al'adarta na haila ba'.

Shaikh Waheed bin Abdus-Salam Baali ya bayyana yadda ake zargin wannan nau'in sihiri yana faruwa, ta hanyar danganta shi da shigar aljani da kuma jawo zubar jini ga macen da aka yi wa sihiri.

ALAMOMIN DA AKE GANE SIHIRIN ZUBAR JINI GA MACE

1. النَّزِيفُ الْمُسْتَمِرُّ

Zubar jini mai ɗorewa.

Wato mace ta ci gaba da fitar da jini daga mahaifarta lo gabanta na tsawon lokaci, musamman idan jinin ya wuce kwanakin hailarta na al'ada ko kuma yana zuwa a lokutan da ba su dace da al'adarta ba.

2. النَّزِيفُ بَعْدَ انْقِطَاعِ الْحَيْضِ

Zubar jini bayan an ɗauka haila ta ƙare.

Wato mace ta ga jini bayan kwanakin hailarta sun wuce, ko kuma jinin ya ci gaba da zuwa bayan lokacin da ta saba ganin tsarki.

3. كَثْرَةُ الدَّمِ النَّازِلِ

Yawan jinin da yake zuba.

Wato jinin da yake fitowa ya kasance yana da yawa fiye da yadda mace ta saba gani, har ya sa ta riƙa sauya kayan kariya akai-akai.

4. تَكَرُّرُ النَّزِيفِ

Maimaita zubar jini.

Wato mace ta riƙa samun zubar jini sau da dama a lokuta daban-daban, ba tare da sanin ainihin dalilin da ya sa hakan yake faruwa ba.

5. طُولُ مُدَّةِ النَّزِيفِ

Tsawaitar lokacin zubar jini.

Wato jinin ya ci gaba da zuwa na kwanaki masu yawa fiye da yadda mace ta saba, ko kuma ya kasance yana dawowa akai-akai.

6. النَّزِيفُ بَيْنَ الدَّوْرَاتِ الشَّهْرِيَّةِ

Zubar jini tsakanin haila da haila.

Wato mace ta ga jini a tsakanin lokutan hailarta na wata-wata, ba tare da kasancewa lokacin hailarta da ta saba ba.

7. النَّزِيفُ بَعْدَ الْجِمَاعِ

Zubar jini bayan saduwa.

Wato mace ta lura cewa jini yana fitowa daga farjinta bayan saduwa.

8. فَقْدَانُ الدَّمِ وَالضَّعْفُ الْعَامُّ

Rashin jini da raunin jiki.

Wato mace ta fara jin kasala, raunin jiki, jiri ko bugun zuciya da sauri sakamakon yawan zubar jini da kuma yiwuwar raguwar jinin da ke jikinta.

Waɗannan alamomi ne da aka ambata daga littafin 'Assarimul battar' na Malamin Sunnah Sheikh Wahid Abdus-Salam Bali', waɗanda suke tabbatar da samuwar sihirin zubar jini ga mace.

Don haka, idan mace tana fama da zubar jini mai yawa, zubar jinin da ba ya tsayawa, jiri mai tsanani, suma, ko ciwon ciki mai tsanani, ya kamata ta garzaya asibiti cikin gaggawa. Idan ba gano matsalar ba sa a haɗa da Malaman ruƙiyya ta Alƙur'ani da Sunnah, da addu'a da neman taimakon Allah, ba tare da neman taimakon Shaiɗanu ba

WASU DAGA CIKIN HANYOYIN NEMAN WARAKA DA KARIYA

Na ɗaya (1): Yin ruƙiyya ta Alƙur'ani da Sunnah.

Musulmi zai iya yi wa kansa ko wani mara lafiya ruƙiyya ta hanyar karanta ayoyin Alƙur'ani da addu'o'in da aka tabbatar daga Annabi ﷺ, yana neman waraka daga Allah Maɗaukakin Sarki.

Daga cikin abin da za a karanta akwai:

* Suratul Fātiha.

* Ayatul Kursiyyu, Suratul Baƙara aya ta 255.

* Ayoyi biyu na ƙarshe na Suratul Baƙara, aya ta 285 zuwa 286.

* Suratul Ikhlās, Suratul Falaƙ da Suratun Nās.

* Addu'o'in neman lafiya da kariya da aka tabbatar daga Annabi ﷺ.

Ana yin ruƙiyya tare da kyakkyawar niyya, dogaro ga Allah da tabbatar da cewa waraka tana hannunSa.

Na biyu (2): Neman kulawar likita.

Idan mace tana zubar da jini na tsawon lokaci, ya kamata ta je asibiti domin a gano dalilin da ya haddasa zubar jinin, a duba ko akwai matsalar mahaifa, ƙarancin jini, matsalar ciki ko wani yanayi da ke bukatar magani.

Na uku (3): Yawaita addu'a da neman lafiya.

Musulmi ya riƙa roƙon Allah Ya ba shi lafiya, Ya yaye masa damuwa, Ya sauƙaƙa masa wahala, tare da kiyaye salloli da azkāran safe da yamma.

Na huɗu (4): Haɗa ruƙiyya da maganin da ya dace.

Ana iya haɗa ruƙiyya ta shari'a da maganin islamic Chemist ko na gargajiya da ya dace da cutar. Idan mace tana son amfani da magungunan Musulunci ko na gargajiya, ya kamata ta tabbatar da cewa suna da aminci, kuma ba za su cutar da ita ko su hana ta samu

n maganin da ya dace ba.

Daga shafin Bashir Halilu, mai Ruƙiyya da bayar da magunguna na Musulunci da na gargajiya.

More from TimesPosts

SIHIRIN SAKAWA MACE ZUBAR JINI | TimesPosts