Skip to content
TimesPosts homeTimesPostsThe record, as it happens.

Shin Ko maine Dalili ... ?

A karo na 2 Najeriya ta yi bikin ’yancin kai ba tare da faretin sojoji baGwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta gudanar da bikin cikar Najeriya shekaru 66 da samun ’yancin kai ba tare da faretin…

Ay Abdullahi · Admin

· 1 min read

A karo na 2 Najeriya ta yi bikin ’yancin kai ba tare da faretin sojoji ba

Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta gudanar da bikin cikar Najeriya shekaru 66 da samun ’yancin kai ba tare da faretin sojoji ba, karo na biyu a jere.

A shekarar 2025 ma gwamnatin ta soke faretin sojojin, inda ta ce hakan ba ya rage muhimmancin bikin ranar ’yancin kai.

Hakan ya zo ne a lokacin da aka kama wasu jami’an soja bisa zargin hannu a wani shirin kifar da gwamnati.

A farkon shekarar 2026, Hedikwatar Tsaro ta tabbatar da cewa bincike ya gano wasu jami’an da ake zargi da hannu a shirin kifar da gwamnati, inda ta ce wadanda bincike ya tabbatar suna da abin amsawa za su fuskanci shari’ar soja.

Sai dai gwamnatin ba ta bayyana cewa rashin gudanar da faretin bana na da alaka da zargin juyin mulki ba.

A maimakon faretin sojoji, an gudanar da wasu shirye-shirye da suka hada da sallar Juma’a, ibadar coci, lacca kan ranar ’yancin kai da kuma jawabin Shugaba Tinubu ga ’yan Najeriya.

More from TimesPosts