Wasu Muhimman Batutuwa Da Mai Girma Shugaban Kasar Nigeria Yayi A Ranar Da Kasar Tasamu Yanchi Dr Ahmad Bola Tinubu
Muhimman abubuwa 10 da ke cikin jawabin Tinubu na ranar ƴancin kai1. Tattalin arziki ya fara samun ci gaba: Ya ce tattalin arzikin Najeriya ya samu bunƙasa da sama da kashi 4% a shekarar 2026.2.…
Ay Abdullahi · Admin
· 1 min read

Muhimman abubuwa 10 da ke cikin jawabin Tinubu na ranar ƴancin kai
1. Tattalin arziki ya fara samun ci gaba: Ya ce tattalin arzikin Najeriya ya samu bunƙasa da sama da kashi 4% a shekarar 2026.
2. Saukar hauhawar farashi: Ya ce hauhawar farashi (inflation) ta ragu sosai idan aka kwatanta da kololuwar matakin da ta kai a baya.
3. Ƙaruwa a ajiyar kuɗaɗen waje: Ya ce Najeriya ta sake gina ajiyar kuɗaɗen ƙetare (foreign reserves).
4. Daidaituwar kasuwar canjin kuɗi: Ya ce kasuwar musayar kuɗaɗen ƙetare ta samu kwanciyar hankali.
5. Karuwar fitar da kayayyakin da ba na man fetur ba: Najeriya ta samu sama da dala biliyan 6 daga fitar da kayayyakin da ba na man fetur ba a shekarar 2025, wanda ya ce shi ne mafi girma a tarihin ƙasar.
6. Raguwar satar danyen mai: Ya bayyana cewa an samu raguwar satar man fetur, lamarin da ya taimaka wajen ƙara samun kuɗaɗen shiga ga ƙasa.
7. Alƙawarin rage tsadar rayuwa: Ya yi alƙawarin samar da abinci mai araha, sauƙaƙa sufuri, inganta wutar lantarki da samar da ayyukan yi.
8. Bunƙasa noma da ababen more rayuwa: Ya yi alkawarin ƙara amfani da injinan noma da inganta hanyoyi, layukan dogo, tashoshin jiragen ruwa da hanyoyin jigilar kayayyaki.
9. Ƙarfafa masana'antu da kasuwanci: Ya ce gwamnati za ta tallafa wa masana'antu, amfani da iskar gas wajen samar da makamashi, da kuma inganta hanyoyin sadarwar zamani.
10. Yaƙi da talauci: Ya amince cewa har yanzu jama'a na fama da tsadar rayuwa, amma ya ce manufar gwamnati ita ce kawar da talauci ba kawai sarrafa shi ba.
More from TimesPosts

Shin Ko maine Dalili ... ?
A karo na 2 Najeriya ta yi bikin ’yancin kai ba tare da faretin sojoji baGwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta gudanar da bikin cikar Najeriya shekaru 66 da samun ’yancin kai ba tare da faretin…
Ay Abdullahi1 min read

Shin Ko Haka Zatayi Kuwa..?
Shugabannin wasu jam’iyyun adawa a Najeriya sun ƙara kaimi wajen tattaunawa kan samar da ɗan takarar shugaban ƙasa guda ɗaya da zai wakilci ɓangaren adawa a zaɓen 2027.A wani sabon mataki na…
Ay Abdullahi1 min read

828.58bn Budget: Radda Puts Katsina’s Development First.
828.58bn Budget: Radda Puts Katsina’s Development First.Governor Malam Dikko Umar Radda (@dikko_radda) has assented to Katsina State’s ₦828.58 billion 2027 Appropriation Law, setting the stage for…
Ay Abdullahi1 min read