Skip to content
TimesPosts homeTimesPostsThe record, as it happens.

Siyasa Duniya ko Kunsa Mai yake Faruwa A Yanzu A Gabas kuwa .?

HASBUNALLAHU WA NI'IMAL WAKILNaci karo da wani labari da BBC suka wallafa a kan harin da 'yan tawayen Houthi na Kasar Yemen suka kai Saudiyya har zuwa Birnin Makkah da MadinaMai magana da yawun…

Ay Abdullahi · Admin

· 2 min read

HASBUNALLAHU WA NI'IMAL WAKIL

Naci karo da wani labari da BBC suka wallafa a kan harin da 'yan tawayen Houthi na Kasar Yemen suka kai Saudiyya har zuwa Birnin Makkah da Madina

Mai magana da yawun rundunar kawancen Soji da Saudiyya ke jagoranta Turki al-Maliki, yace harin na mayakan Houthi ya lalata tashar rarraba wutar lantarki da ke samar da wuta a Masallacin Manzon Allah Annabi Muhammad (SAW) dake birnin Madinah

Mai magana da yawun kawancen Sojin Turki al-Maliki yace harin an kai shi ne kan tashar rarraba wutar lantarki ta Taibah, inda ya bayyana harin a matsayin “aikin ta’addanci na matsorata”

Al-Maliki yace cibiyar na samar da wutar lantarki ga Masallacin Annabi da ke Madina, daya daga cikin wurare mafi tsarki a Musulunci

Sanarwar ta baya-bayan nan ta zo ne yayin da ake samun jerin hare-haren makamai masu linzami da jirage marasa matuki kan Saudiyya, wadanda ake dangantawa da kungiyar Houthi

Saudiyya tace dakarun kare sararin samaniyarta sun kakkabo tare da lalata wani jirgi mara matuki na Houthi a kudancin Makka, kafin ya shiga sararin samaniyar da aka haramta shiga na birnin mai tsarki. ~Rahoton BBC

Houthi kungiyace ta 'yan tawaye a Kasar Yemen masu bin akidar shi'anci, wanda suke samun tallafin kudi da makamai na ta'addanci daga Kasar Iran, to a cikin kwanakin nan sun matsa da kai hari zuwa Saudiyya

Firaminista na Kasar Pakistan, Shehbaz Sharif, yayi gargadin cewa duk wani hari ko barazanan tsaro da zai shafi Makkah da Madinah zai kasance “jan layi da bai kamata a ketare shi ba”

Firaministan yayi Allah-wadai da hare-haren ’yan Houthi a kan Saudiyyah, ya jaddada cewa Kasar Pakistan zata goyi baya don tsaron wuraren ibada biyu masu tsarki dake Makkah da Madinah da kuma kare lafiyar Mahajjata

Tabbas idan Iran bata daina bawa mayakan Houthi taimakon da suke kai hari Saudiyyah har gurare masu tsarki ba to faduwar Iran yazo, domin Allah ba zai kyale ba

Allah Ka rusa mayakan Houthi da wadanda suke taimakonsu wajen cutar da birnin Makkah da Madinah

More from TimesPosts

Siyasa Duniya A yau | TimesPosts