Tinubu ya ceci tattalin arzikin Najeriya - Shettima
Tinubu ya ceci tattalin arzikin Najeriya - ShettimaMataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya bukaci ’yan Najeriya da su yi wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu uzuri, yana mai cewa matakan da ya dauka…
Ay Abdullahi · Admin
· 1 min read

Tinubu ya ceci tattalin arzikin Najeriya - Shettima
Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya bukaci ’yan Najeriya da su yi wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu uzuri, yana mai cewa matakan da ya dauka sun ceci tattalin arzikin kasar daga durkushewa.
Shettima ya bayyana hakan ne a Legas ranar Asabar, bayan ganawa da Shugaba Tinubu, inda ya ce lokacin da gwamnatin ta karbi mulki, kudaden ajiyar kasashen waje sun kai dala biliyan $3.9 kacal, abin da bai isa shigo da man fetur na wata guda ba.
Ya ce cire tallafin man fetur da hada farashin canjin kudade sun kasance daga cikin tsauraran matakan da Tinubu ya dauka domin farfado da tattalin arzikin kasar.
Shettima ya amince cewa ’yan Najeriya na fuskantar matsin tattalin arziki, amma ya ce mawuyacin hali ba ya dawwama.
Ya kuma ce gwamnatin tarayya na shirin kaddamar da wasu shirye-shirye da suka hada da amfani da babura masu kafa uku masu amfani da wutar lantarki 10,600 a Arewa maso Gabas, tare da tura motocin bas 300 da e-taxis domin rage radadin tsadar sufuri.
Mataimakin shugaban kasar ya kuma bayyana Asusun Ba da Lamunin Ilimi na Najeriya (NELFUND) a matsayin wani muhimmin shiri da ke taimaka wa dalibai daga iyalai masu karamin karfi.
A cewarsa, gwamnatin Tinubu za ta ci gaba da gudanar da mulki tare da shiga harkokin siyasa yayin da ake tunkarar babban zaben 2027.
More from TimesPosts

Siyasa Duniya A Yau. MUMMUNAR ZANGA-ZANGAR TA RINCABE A P@KISTAN
MUMMUNAR ZANGA-ZANGAR TA RINCABE A P@KISTAN Yanzu haka magoya bayan wannan mashahuran mutumin na P@kistan IMRAN Kh@n sun fara zanga-zangar dole a sake shi .Imran Khan shi ne tsohon Firayim Ministan…
Ay Abdullahi1 min read

White House news
“I am announcing the formation of the Super Intelligence Force (SIF). The Super Intelligence Force is tasked with coordinating the effort of the Federal Government to ensure that America continues to…
Ay Abdullahi1 min read

America Did Not Gain Power Through Democracy.
America Did Not Gain Power Through Democracy.In the 1950s, South Korea was among the poorest countries in the world. But later it experienced a tremendous transformation, becoming a country with…
Ay Abdullahi3 min read