Ƴansanda sun gayyaci ɗan takarar NDC, Aminu Warkal kan zargin fito da bindiga a taron siyasa
Ƴansanda sun gayyaci ɗan takarar NDC, Aminu Warkal kan zargin fito da bindiga a taron siyasaRundunar ’yansandan Jihar Kano ta gayyaci ɗan takarar jam’iyyar NDC, Hon. Aminu Abdullahi Warkal, domin yi…
Ay Abdullahi · Admin
· 1 min read

Ƴansanda sun gayyaci ɗan takarar NDC, Aminu Warkal kan zargin fito da bindiga a taron siyasa
Rundunar ’yansandan Jihar Kano ta gayyaci ɗan takarar jam’iyyar NDC, Hon. Aminu Abdullahi Warkal, domin yi masa tambayoyi kan zargin nuna bindiga a bainar jama’a.
Rundunar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da kakakinta, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar ranar Litinin, 5 ga Oktoba, 2026.
A cewar sanarwar, rundunar ta ci karo da wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta yayin da take sintirin sa ido a yanar gizo, inda ake zargin an ga Warkal yana nuna wata bindiga da ake kyautata zaton bindigar Pump Action.
Rundunar ta ce idan aka tabbatar da zargin, hakan na iya zama keta dokar mallakar bindigogi ta Firearms Act, tare da haddasa tsoro da fargaba da kuma barazana ga zaman lafiyar jama’a.
Sanarwar ta ce an gayyaci Warkal zuwa hedikwatar rundunar da ke Bompai, Kano, bisa umarnin Kwamishinan ’yansandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori.
A halin yanzu, ɗan takarar na NDC yana hannun sashen leƙen asiri na rundunar (SID), inda ake ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.
Kwamishinan ’yansandan ya yi gargadin cewa rundunar ba za ta lamunci duk wani nau’in rashin bin doka, daba ko nuna makamai da ka iya barazana ga zaman lafiyar jama’a ba, ba tare da la’akari da matsayin wanda abin ya shafa ba.
Ya kuma shawarci ’yan takara, magoya bayansu da sauran masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa da su gudanar da ayyukansu cikin lumana tare da bin tanade-tanaden Dokar Zabe, Dokar Makamai da sauran dokokin ƙasa.
Rundunar ta sake jaddada kudirinta na kare rayuka da dukiyoyin jama’a da kuma tabbatar da zaman lafiya a Jihar Kano kafin, lokacin da kuma bayan kakar siyasa.
More from TimesPosts

Wani Farfesa daga Japan ya ce... Zan yi maka tambayoyi 9 masu wahala, waɗanda za su taimaka maka ka fahimci kanka fiye da yadda kake zato.
Wani Farfesa daga Japan ya ce... Zan yi maka tambayoyi 9 masu wahala, waɗanda za su taimaka maka ka fahimci kanka fiye da yadda kake zato.1. Idan aka ce saura kwana ɗaya kacal ka kwananka ya kare...…
Ay Abdullahi1 min read

Abubuwa 5 Mafiya Ban Tsoro Da Masana Kimiyya Suka Gano A Teku Amma Na Ƙarshe Shi Ne Zai Sa Ka Tunani.
Abubuwa 5 Mafiya Ban Tsoro Da Masana Kimiyya Suka Gano A Teku Amma Na Ƙarshe Shi Ne Zai Sa Ka Tunani.A wani wuri a ƙarƙashin Gulf of Mexico, akwai wani tafki mai ɗauke da ruwan gishiri mai tsananin…
Ay Abdullahi2 min read

SABBIN IYAYE KU KOYI HAƘURI
SABBIN IYAYE KU KOYI HAƘURI Haihuwa ɗaukaka ce, bakuwa a samun daukaka sai anjure, iyayen mu nada shiri suke mata na gaske, shiyasa wata saita gama naƙuda ta haihu ɗaki daya ga mijinta yana Bacci…
Ay Abdullahi3 min read