Labaran Duniya ::::: Amnesty ta buƙaci a binciki barazanar kisa da ake yi wa Abdul Turaki
Amnesty ta buƙaci a binciki barazanar kisa da ake yi wa Abdul TurakiƘungiyar kare haƙƙin bil'adama ta Amnesty International ta buƙaci hukumomin tsaro a Najeriya su gudanar da bincike cikin gaggawa…
Ay Abdullahi · Admin
· 2 min read

Amnesty ta buƙaci a binciki barazanar kisa da ake yi wa Abdul Turaki
Ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama ta Amnesty International ta buƙaci hukumomin tsaro a Najeriya su gudanar da bincike cikin gaggawa kan barazanar kisa da ake zargin ana yi wa mai sharhi a kafafen sada zumunta, Abdul Turaki.
Haka kuma, ƙungiyar ta bukaci a samar masa da kariya domin tabbatar da tsaron rayuwarsa.
Amnesty ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Alhamis, inda ta ce tana matuƙar damuwa da jerin barazanar kisa da zagi, da kuma barazanar amfani da ƙarfin ikon gwamnati wajen kawar da shi.
Ƙungiyar ta ce barazanar ta biyo bayan fallasa wasu zarge-zargen mu'amalar siyasa da Turaki ya yi, waɗanda suka shafi ɗan Shugaba Bola Tinubu, Seyi Tinubu, da mai sharhi a kafafen sada zumunta, Dan Bello, dangane da babban zaɓen 2027.
A ranar Laraba, 25 ga Nuwamba, Turaki ya fitar da wani bidiyo inda ya bayyana cewa rayuwarsa na cikin haɗari sakamakon bayanan da ya fallasa game da zargin wasu mu'amalolin siyasa da suka shafi jam'iyyar APC mai mulki.
Amnesty ta ce dole ne hukumomin tsaro su ɗauki zarge-zargen da muhimmanci tare da gaggauta gudanar da bincike.
“Ya zama wajibi a wannan lokaci hukumomin tsaro su binciki zarge-zargen Abdul Turaki cikin gaggawa da kuma muhimmancin da suka dace,” in ji ƙungiyar.
Ta ƙara da cewa ya kamata a ba shi kariya, musamman ganin yadda wasu daga cikin barazanar ke nuna cewa waɗanda ke yi masa barazanar na iya bin sawunsa tare da cutar da shi ba tare da fuskantar hukunci ba.
Sai dai Amnesty ba ta bayyana sunayen mutanen da ake zargi da yi wa Turaki barazanar ba, haka kuma ba ta tabbatar da ko ya shigar da ƙorafi a hukumance ga jami'an tsaro ba.
Haka nan, ba a bayyana ko hukumomin tsaro sun fara gudanar da bincike ko kuma sun samar masa da wata kariya ba.
Ƙungiyar ta yi gargaɗin cewa barazanar amfani da ƙarfin siyasa ko ikon gwamnati wajen tsoratar da masu sukar lamuran jama'a abu ne da bai kamata hukumomi su yi watsi da shi ba.
Ta kuma jaddada cewa dole ne a tabbatar da cewa Turaki na iya amfani da 'yancinsa na faɗar albarkacin baki ba tare da fargabar cin zarafi ko barazanar rasa ransa ba.
More from TimesPosts

Labaran Duniya. ::: IRAN TA RIKITA AMURKA GABADAYA 😂
IRAN TA RIKITA AMURKA GABADAYA 😂Tsohon Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Antony Blinken, ya bayyana cewa hanya daya tilo da Amurka za ta iya cin nasara ga Iran ita ce kai mata farmakin sojojin kasa,…
Ay Abdullahi1 min read

Labaran chiki Gida Nigeria. :: Sarki Sanusi ya kai ziyara ga Olubadan a Ibadan don ƙarfafa alaƙar Hausawa da Yarabawa
Sarki Sanusi ya kai ziyara ga Olubadan a Ibadan don ƙarfafa alaƙar Hausawa da YarabawaMai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya kai ziyara fadar Olubadan na Ibadan, Oba Rashidi Ladoja, domin…
Ay Abdullahi1 min read

Labaran Duniya ::: Yau Shekaru 79 da Tarayyar Soviet ta kammala samar da AK-47, daya daga cikin manyan bindigogin kai hari na farko
Yau Shekaru 79 da Tarayyar Soviet ta kammala samar da AK-47, daya daga cikin manyan bindigogin kai hari na farkoA Ranar 13 Ga Watan Nuwamba 1947 Tarayyar Soviet ta kammala samar da AK-47, daya daga…
Ay Abdullahi3 min read