Skip to content
TimesPosts homeTimesPostsThe record, as it happens.

Labaran Duniya. ::: IRAN TA RIKITA AMURKA GABADAYA 😂

IRAN TA RIKITA AMURKA GABADAYA 😂Tsohon Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Antony Blinken, ya bayyana cewa hanya daya tilo da Amurka za ta iya cin nasara ga Iran ita ce kai mata farmakin sojojin kasa,…

Ay Abdullahi · Admin

· 1 min read

IRAN TA RIKITA AMURKA GABADAYA 😂

Tsohon Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Antony Blinken, ya bayyana cewa hanya daya tilo da Amurka za ta iya cin nasara ga Iran ita ce kai mata farmakin sojojin kasa, amma ko hakan ma zai zama babban bala'i ga Amurka.

Ya ce:

"Kasar Iran ta fi jihar California ta Amurka girma sau hudu. Ta fi Iraki girma sau uku, kuma tana da al'umma kimanin mutum miliyan 90.

Gabar tekun Iran da ke kan mashigar ruwan Hormuz tana da matukar tsawo. Makaman da take ci gaba da kerawa kuwa, tana boye su ne a wurare masu nisa, kuma karfinsu da zangon harbinsu ya yi yawa. Saboda haka, ba zai yiwu kawai a lalata dukkan makamanta ta hanyar hare-haren sama ba.

Wata kila sai an kai mata farmakin sojojin kasa domin cimma wannan buri, amma hakan zai zama babban bala'i ga Amurka."

More from TimesPosts