Skip to content
TimesPosts homeTimesPostsThe record, as it happens.

Breaking News : Labaran Duniya Na Gabashin Duniya

LABARI MARAR DADIGwamnatin Kasar Saudiyya ta sanar da rufe filin jirgin saman kasa da kasa na Sarki Khalid bin Abdul-Aziz dake birnin Riyadh sakamakon mummunan hari na ta'addanci da mayakan Houthi…

Ay Abdullahi · Admin

· 2 min read

LABARI MARAR DADI

Gwamnatin Kasar Saudiyya ta sanar da rufe filin jirgin saman kasa da kasa na Sarki Khalid bin Abdul-Aziz dake birnin Riyadh sakamakon mummunan hari na ta'addanci da mayakan Houthi suka kaddamar a filin jirgin

Harin ya cinye rayukan mutane 12,mutane 309 sun samu munanan raunuka, daga cikin wadanda suka mutu akwai ’yan Saudiyya 4, ’yan Kasar Bangladesh 2, dan Kasar Amurka 1, dan Kasar Falasdinu 1, dan Kasar Jordan 1, dan Kasar Syria 1, dan Kasar Sudan 1, sai dan Kasar Masar 1

Wani makami mai linzami da mayakan Houthi suka harba shine ya bugi tashar fasinjojin filin jirgin saman Sarki Khalid, inda wani bangare na rufin gini ya rufta kan mutane kusa da kofar tashin jiragen sama na filin jirgin

Yanzu haka mahukuntan Saudiyya sun tabbatar da rufe filin jirgin saman, an karkatar da jiragen sama zuwa wasu filayen jiragen sama, sannan kamfanonin jiragen sama suna ta soke tashin jiragensu zuwa Saudiyya

Wannan shi ne hari na uku da aka kai kan filin jiragen saman Riyadh, kungiyar 'yan ta'addan Houthi mai samun goyon bayan Iran ta ayyana sararin samaniyar Saudiyya da filayen jiragen Kasar Saudiyya a matsayin gurin da makamanta masu linzami zasu yi ta shawagi

Saudiyya ta kashe biliyoyin daloli wajen sayen jiragen yakin Amurka, makaman kariya masu linzami na Patriot da tsarin THAAD, amma Houthi suna amfani da makamai masu linzami masu bin tafarkin ballistic da jiragen yaki marasa matuka (drones) domin kauce wa wadannan tsare-tsaren kariya na Saudiyya

Houthi suna iko da gabar tekun Bahar Maliya ta Kasar Yemen, suna kuma iko da mashigar ruwa ta Bab al-Mandab, sun dakatar da fitar da man fetur din Saudiyya ta hanyar Bahar Maliya, yanzu kuma suna kai hari kan babban birnin Kasar Saudiyya Riyadh

Yakin ya sauya alkibla, Saudiyya ba ita ce ke farautar abokan gaba ba yanzu; ita ce ake farautar ta, me zai faru idan Kasar Saudiyya da take da rundunar Sojin sama mafi inganci a yankin gabas ta tsakiya ta kasa kare filin jiragen saman babban birninta?

Hakan yana nufin da wahala a gudanar da aikin Hajji na wannan shekara idan duniya batayi taron dangi an ragargaji tsinannun nan mayakan Houthi ba

Yaa Allah Ka kare Kasar Saudiyya, Allah Ka nuna mana karshen mayakan Houthi

More from TimesPosts