Skip to content
TimesPosts homeTimesPostsThe record, as it happens.

BUNKASA FILIN JIRGIN MALAM AMINU KANO ZAI HABAKA TATTALIN ARZIKIN AREWA.

BUNKASA FILIN JIRGIN MALAM AMINU KANO ZAI HABAKA TATTALIN ARZIKIN AREWA.Masu ruwa da tsaki kan harkokin shigo da fitar da kayayyaki ta filin jirgin saman Malam Aminu Kano sun bayyana cewa bunkasa…

Ay Abdullahi · Admin

· 1 min read

BUNKASA FILIN JIRGIN MALAM AMINU KANO ZAI HABAKA TATTALIN ARZIKIN AREWA.

BUNKASA FILIN JIRGIN MALAM AMINU KANO ZAI HABAKA TATTALIN ARZIKIN AREWA.

Masu ruwa da tsaki kan harkokin shigo da fitar da kayayyaki ta filin jirgin saman Malam Aminu Kano sun bayyana cewa bunkasa filin jirgin zai taimaka matuka wajen habaka tattalin arzikin Jihar Kano da sauran jihohin Arewa, musamman ta hanyar saukaka safarar kayayyaki da bunkasa harkokin kasuwanci zuwa cikin gida da kasashen ketare.

Sun bayyana hakan ne yayin da suka kai ziyara ga Shugaban Majalisar Gudanarwa ta Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama ta Najeriya, FAAN, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, domin yaba masa kan rawar da ya taka wajen jawo hankalin Gwamnatin Tarayya game da bukatar bunkasa da inganta filin jirgin saman Malam Aminu Kano.

Tawagar, karkashin jagorancin Shugabanta Muftahu Ya’u, tare da Babban Mataimakin Daraktan Hukumar Kula da Tattalin Arzikin Tashoshin Shige da Fitar da Kayayyaki ta Kasa na shiyyar Arewa maso Yamma, Muhammad Audu, ta bayyana jin dadinta kan shirin gyaran filin jirgin, wanda aka kiyasta kudinsa da kimanin naira biliyan arba’in da shida. Sun ce aikin zai inganta ayyukan filin jirgin tare da kara saukaka zirga-zirgar jiragen sama da harkokin kasuwanci.

A yayin ziyarar, tawagar ta kuma yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta kammala babban tashar shige da fitar da kayayyaki ta kasa da kasa da ake ginawa a filin jirgin saman Malam Aminu Kano, tana mai cewa hakan zai kara inganta harkokin safarar kayayyaki tare da rage wahalhalun da ’yan kasuwa ke fuskanta wajen shigo da kaya da fitar da su zuwa kasashen waje.

Wakilinmu Murtala Abdullahi Baba ya rawaito cewa Muftahu Ya’u da Muhammad Audu sun ce kammala tashar da kuma bunkasa filin jirgin zai kara wa Kano damar zama muhimmiyar cibiyar harkokin kasuwanci da safarar kayayyaki a Arewa, tare da jawo karin masu zuba jari da bude sabbin hanyoyin bunkasa tattalin arzikin yankin.

More from TimesPosts

BUNKASA FILIN JIRGIN MALAM AMINU KANO ZAI HABAKA TATTALIN ARZIKIN AREWA. | TimesPosts