Mafi darajar kuɗi a Africa ba Naira ba ce. Ba CFA Franc na Nijar ba ne. Ba Rand na South Africa ba ne. Kuma ba Cedi na Ghana ba
Mafi darajar kuɗi a Africa ba Naira ba ce. Ba CFA Franc na Nijar ba ne. Ba Rand na South Africa ba ne. Kuma ba Cedi na Ghana ba ne.Idan na tambaye ka wace ƙasa ce take da kuɗin da ya fi daraja a…
Ay Abdullahi · Admin
· 3 min read

Mafi darajar kuɗi a Africa ba Naira ba ce. Ba CFA Franc na Nijar ba ne. Ba Rand na South Africa ba ne. Kuma ba Cedi na Ghana ba ne.
Idan na tambaye ka wace ƙasa ce take da kuɗin da ya fi daraja a Africa, wataƙila hankalinka zai tafi kai tsaye zuwa South Africa, saboda Rand ɗinta ya shahara sosai. Ko kuma Nigeria, saboda girman tattalin arzikinta. Wasu kuma za su ce Kenya.
Amma abin mamaki shi ne, amsar tana wani wuri da mutane da yawa ba za su yi tsammani ba.
Akwai abu ɗaya da ya kamata mu fara fahimta. Kuɗi mai daraja ba yana nufin ƙasar ta fi kowace ƙasa arziki ba.
Abin da ake aunawa a nan shi ne ƙimar unit ɗin kuɗin ƙasa idan aka kwatanta da Dalar Amurka, ba girman tattalin arzikinta ko yawan arzikin da talakawanta suke da shi ba.
Misali, akwai kuɗin ƙasashen Africa da unit ɗinsu yake da ƙima sosai idan aka kwatanta da Dollar, amma hakan kaɗai ba ya nufin tattalin arzikin ƙasar ya fi na kowace ƙasa girma.
Daga cikin kuɗaɗen da suke kan gaba akwai Namibian Dollar da Lilangeni na Eswatini, waɗanda suke da alaƙa da South African Rand.Sai Rand ɗin South Africa kansa.
Abin mamaki kuma shi ne, duk yadda Rand ya shahara a Africa, ba shi ne mafi daraja ba.
Sai kuma Nakfa na Eritrea, wanda ke da wani abu na musamman. Gwamnatin ƙasar tana da tsauraran matakai wajen sarrafa kuɗinta, don haka official exchange rate ba lallai ya kasance daidai da abin da ake samu a kasuwa ba.
Daga nan akwai Pula na Botswana, wanda tattalin arzikinta ya samu gagarumar gudummawa daga harkar lu’u-lu’u da kuma wasu manufofin tattalin arzikin ƙasar.
Akwai kuma Rupee na Seychelles, inda yawon buɗe ido ke kawo wa ƙasar kuɗaɗen waje masu yawa. Amma har yanzu ba nan abin zai ba da sha’awa ba.
Domin akwai wata ƙasa da kuɗinta ya taɓa fuskantar mummunar faɗuwa, amma daga baya ya samu gagarumar farfadowa a 2025 zuwa 2026.
Ghana.... Cedi ɗinta ya sake samun matsayi mai ƙarfi a wannan ma’aunin, wanda ya taimakawa Ghana ta shiga cikin ƙasashen da kuɗaɗensu suke da babban nominal value a Africa. Amma duk da haka, ba ita ce ta farko ba.
Bari mu koma Arewacin Africa. A can abubuwa sun fi ban sha’awa. Morocco tana da Dirham. Libya kuma tana da Dinar.
Libya tana da wani abin mamaki. Duk da matsalolin siyasar da ta fuskanta, Dinar ɗinta yana daga cikin kuɗaɗen Africa masu babban nominal value. Man fetur da kuma tsarin musayar kuɗin ƙasar suna daga cikin abubuwan da ke tasiri sosai.
Har yanzu dai muna neman wacce take a matsayi na ɗaya. Kuma ga abin da zai iya baka mamaki. Ba Nigeria ba ce. Ba South Africa ba ce. Ba Ghana ba ce. Ba Libya ba ce. Ba Morocco ba ce. To, wace ƙasa ce?
Tunisia.... Tunisian Dinar ne yake da mafi girman nominal value a Africa idan aka kwatanta da Dalar Amurka a wannan ma’auni. A 2026, kusan Dinar 3 kacal ake buƙata domin samun US$1.
Amma kada ka tsaya iya haka ka ce... Kenan Tunisia ta fi Nigeria ko South Africa ƙarfin tattalin arziki? A’a.
Wannan shi ne babban darasin da mutane da yawa suke rasa... Ƙimar kuɗi da ƙarfin tattalin arziki abubuwa biyu ne daban.
Ƙasar da kuɗinta ya fi daraja ba lallai ta kasance ita ce ta fi kowa yawan arziki, masana’antu, albashi ko ƙarfin tattalin arziki ba.
Ga kuma wasu tambayoyin da zan barka dasu da baka da amsar su.
Me ya sa Dalar Amurka ce muke amfani da ita wajen auna kusan dukkan waɗannan kuɗaɗe?
Ta yaya Dollar ta zama babban ma’aunin da duniya ke amfani da shi?
Kuma shin Africa za ta iya samun tsarin kuɗi wanda zai rage dogaro da Dollar a nan gaba?
Idan wannan rubutun ya ƙara maka ilimi, to ni na cika aikina.
Sources: IMF, World Bank, African Development Bank, da bayanan bankunan ƙasashe.
#DigitalPsychologist @topfans
More from TimesPosts

BUNKASA FILIN JIRGIN MALAM AMINU KANO ZAI HABAKA TATTALIN ARZIKIN AREWA.
BUNKASA FILIN JIRGIN MALAM AMINU KANO ZAI HABAKA TATTALIN ARZIKIN AREWA.Masu ruwa da tsaki kan harkokin shigo da fitar da kayayyaki ta filin jirgin saman Malam Aminu Kano sun bayyana cewa bunkasa…
Ay Abdullahi1 min read

Shin Ko Kunsan Suma Haka Ta Faru Dasu Kuwa.....?
China da India duk sun taɓa fama da matsanancin talauci. Amma me ya sauya komai cikin shekaru 40?A shekarun 1980s, China da India suna cikin ƙasashen da ke fama da matsanancin talauci. Amma bayan…
Ay Abdullahi1 min read

DO YOU UNDERSTAND HOW MONEY WORKS?
DO YOU UNDERSTAND HOW MONEY WORKS?Do you really understand how money works?Here are 5 things yo
Ay Abdullahi2 min read