Skip to content
TimesPosts homeTimesPostsThe record, as it happens.

Kasuwanchi. ::: Hadada Hannu Jari Dangote zai ƙara jari zuwa Dala biliyan 70 don bunƙasa kasuwancin sa a faɗin Afirka

Dangote zai ƙara jari zuwa Dala biliyan 70 don bunƙasa kasuwancin sa a faɗin AfirkaAttajirin ɗan kasuwa Aliko Dangote ya bayyana shirin ƙara zuba hannun jarin kamfaninsa a Afirka daga dala biliyan 50…

Ay Abdullahi · Admin

· 1 min read

Dangote zai ƙara jari zuwa Dala biliyan 70 don bunƙasa kasuwancin sa a faɗin Afirka

Attajirin ɗan kasuwa Aliko Dangote ya bayyana shirin ƙara zuba hannun jarin kamfaninsa a Afirka daga dala biliyan 50 zuwa biliyan 70 nan da shekarar 2030.

Dangote ya kuma ce yana shirin samar da wutar lantarki mai ƙarfin megawatt 10,000 a faɗin Afirka, ciki har da Najeriya, domin bunƙasa masana’antu da tattalin arzikin nahiyar.

Ya bayyana hakan ne yayin ganawarsa da wasu masu ruwa da tsaki a shafukan sada zumunta da ƴan jarida daga Arewacin Najeriya, waɗanda suka ziyarci matatar man Dangote da masana’antar takin zamani da ke Legas ranar Alhamis.

Attajirin ya ce rashin wadatacciyar wutar lantarki na daga cikin manyan matsalolin da ke hana ƙananan masana’antu da matsakaitan ‘yan kasuwa samun ci gaba, musamman saboda tsadar amfani da janareta mai amfani da fetur da dizal.

Ya bayyana cewa a halin yanzu kamfaninsa na samar da kusan megawatt 1,500 na wutar lantarki domin gudanar da ayyukansa, amma ana sa ran ƙarfin zai kai tsakanin megawatt 4,500 zuwa 5,000 bayan kammala shirin Vision 2030.

Dangote ya jaddada cewa samar da ayyukan yi da bunƙasa masana’antu su ne hanyoyin magance matsalolin tattalin arziki da rashin tsaro, yana mai cewa gwamnati na da alhakin samar da kyawawan manufofi da yanayin da zai ba ‘yan kasuwa damar zuba jari.

Ya kuma bukaci Najeriya ta daina dogaro da fitar da albarkatun ƙasa ba tare da sarrafa su ba, yana mai cewa ya kamata a riƙa sarrafa kayayyakin cikin gida kafin fitar da su zuwa ƙasashen waje.

A cewarsa, noma da ma’adanai na daga cikin manyan fannonin da Arewacin Najeriya zai iya cin gajiyarsu idan aka samar da isassun ababen more rayuwa da masana’antun sarrafa albarkatun ƙasa.

More from TimesPosts