Skip to content
TimesPosts homeTimesPostsThe record, as it happens.

Da Dumi-Duminsa: Ankai Harin Bama Bamai Kamfanin Sadarwa na Israela Intel a Birnin Kasar na Tel-Aviv

Da Dumi-Duminsa: Ankai Harin Bama Bamai Kamfanin Sadarwa na Israela Intel a Birnin Kasar na Tel-Aviv Fashewa a Kamfanin Intel, Mutane da Dama Sun Ji Rauni Mai TsananiRahotanni daga kafafen yaɗa…

Ay Abdullahi · Admin

· 1 min read

Da Dumi-Duminsa: Ankai Harin Bama Bamai Kamfanin Sadarwa na Israela Intel a Birnin Kasar na Tel-Aviv

Fashewa a Kamfanin Intel, Mutane da Dama Sun Ji Rauni Mai Tsanani

Rahotanni daga kafafen yaɗa labaran Ibrananci sun bayyana cewa, mutane uku sun samu raunuka masu tsanani sakamakon wani fashewa da ta auku a masana'antar kamfanin fasahar sadarwa ta Intel, da ke birnin Kiryat Gat, kudancin Tel Aviv.

Rahotannin sun ce jami'an agajin gaggawa sun bayyana fargabar yiwuwar malalar wasu sinadarai masu haɗari a wurin, sakamakon fashewar.

Haka kuma, jami'an kashe gobara da ceto sun tabbatar da cewa an tura ƙungiyoyin kashe gobara da ceto guda takwas zuwa wurin domin gudanar da ayyukan ceto da shawo kan lamarin.

Rahotannin farko sun nuna cewa ana ci gaba da binciken musabbabin fashewar da kuma tantance haɗarin da ka iya tasowa daga malalar sinadaran.

More from TimesPosts