Da Dumi-Duminsa:Iran Na Shirin Bayyana Wani Sabon Makami Mai Hatsarin Gaske Da Ta Lakaba Wa Suna “Uban Dukkan Bama-bamai”
Da Dumi-Duminsa:Iran Na Shirin Bayyana Wani Sabon Makami Mai Hatsarin Gaske Da Ta Lakaba Wa Suna “Uban Dukkan Bama-bamai”Kakakin rundunar juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC), Hossein Mohebi, ya…
Ay Abdullahi · Admin
· 1 min read

Da Dumi-Duminsa:Iran Na Shirin Bayyana Wani Sabon Makami Mai Hatsarin Gaske Da Ta Lakaba Wa Suna “Uban Dukkan Bama-bamai”
Kakakin rundunar juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC), Hossein Mohebi, ya bayyana cewa Iran na shirye-shiryen fito da wani sabon makami da ta kira “Father of All Bombs”, wato “Uban Dukkan Bama-bamai”.
Sai dai kakakin bai bayyana irin makamin ba, ko irin ƙarfin da yake da shi, ko kuma lokacin da za a gabatar da shi a hukumance.
Haka kuma, Mohebi ya yi ikirarin cewa yawan makaman linzami da Iran ke da su ya ƙaru da kashi 50 cikin 100 tun bayan yaƙin kwanaki 12 da ta yi da Isra'ila a watan Yunin 2025.
Ya ƙara da cewa Iran ta inganta ƙarfin makaman linzaminta, tsawon zangon da suke iya kaiwa da kuma daidaiton kai hari.
Sai dai har yanzu ba a fitar da bayanan da za su tabbatar da waɗannan ikirari da kansu ba. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da takun-saƙa tsakanin Iran da Amurka ke ƙara tsananta.
More from TimesPosts

Wace ƙasa ce Azerbaijan, ƙasar da ke iyaka da Iran kuma mafi rinjayen al'ummarta ƴan Shi'a, amma suke da kyakkyawar alaƙar difilomasiyya da Isra'ila, amma Iran bata taɓa kai mata farmaki ba?
Wace ƙasa ce Azerbaijan, ƙasar da ke iyaka da Iran kuma mafi rinjayen al'ummarta ƴan Shi'a, amma suke da kyakkyawar alaƙar difilomasiyya da Isra'ila, amma Iran bata taɓa kai mata farmaki ba?Ga…
Ay Abdullahi2 min read

Wai Ko Kunsan Mai Yake Faruwa A France Kuwa.....?
Hausawa kance wai "A GARGADI MAI GINA RAMIN MUGUNTA"Biyo bayan gagarumar zanga-zangar da aka gudanar a Faransa kan tsadar rayuwa da tabarbarewar ayyukan jama’a, wasu masu tarzoma sun ƙona wani…
Ay Abdullahi1 min read

Dakta Mahsa Taheri, ƙwararriyar masaniyar kimiyyar kera makamai masu linzami ta Iran, wadda ta yi shahada.
Dakta Mahsa Taheri, ƙwararriyar masaniyar kimiyyar kera makamai masu linzami ta Iran, wadda ta yi shahada.Wata matashiya ce da aka haifa a birnin Arak a shekarar 1993. A nan ne ta yi karatun farko a…
Ay Abdullahi1 min read