Interpol ta kama ƴan Najeriya biyu kan zargin damfarar Intanet ta Dala Miliyan 2.4
Interpol ta kama ƴan Najeriya biyu kan zargin damfarar Intanet ta Dala Miliyan 2.4Hukumar ƴansandan kasa da kasa (Interpol) ta kama ’yan Najeriya biyu bisa zargin hannu a laifukan intanet, ciki har…
Ay Abdullahi · Admin
· 1 min read

Interpol ta kama ƴan Najeriya biyu kan zargin damfarar Intanet ta Dala Miliyan 2.4
Hukumar ƴansandan kasa da kasa (Interpol) ta kama ’yan Najeriya biyu bisa zargin hannu a laifukan intanet, ciki har da damfarar zuba jari ta dala miliyan 2.4.
Interpol ta bayyana cewa kamen ya biyo bayan wani samame mai suna Operation Serengeti III, wanda aka gudanar daga ranar 29 ga Yuni zuwa 31 ga Agusta, 2026, tare da haɗin gwiwar hukumomin tsaro na ƙasashen Afirka 20 da Amurka.
A cewar sanarwar da hukumar ta wallafa, an kama mutum 1,462, tare da wargaza hanyoyin aikata laifukan intanet guda 10,909 da kuma kwato kuɗaɗen haram da suka kai dala miliyan 105.
A Najeriya, an kama wani mutum da ake zargi da gudanar da damfarar intanet ta hanyar satar bayanan shiga manhajoji, inda ya tattara adireshin imel kusan miliyan 2.1. Hukumomi sun kuma ƙwato wata mota alfarma da ake zargin an saya da kuɗaɗen laifuka.
Haka kuma, an kama wani mutum kan zargin hannu a wata damfarar zuba jari ta ƙasa da ƙasa da ake tallatawa ta manhajojin saƙonni. Bincike ya nuna cewa an tura kuɗaɗen da ake zargin haramun ne da suka haura dala miliyan 2.4, waɗanda aka karkatar da yawancinsu ta hanyar hada-hadar kuɗaɗen kirifto.
Interpol ta ce samamen na da nufin yaƙi da damfarar intanet, satar bayanan kasuwanci ta imel, kai hare-haren yanar gizo, da kuma karɓar kuɗi ta hanyar barazana.
Hukumar ta ƙara da cewa ƙasashen da suka shiga aikin sun haɗa da Najeriya, Ghana, Kenya, Uganda, Afirka ta Kudu da sauran ƙasashen Afirka.
More from TimesPosts

Labaran Duniya :: YAKIN NUKILIYA.
YAKIN NUKILIYA.Ana sa ran sake barkewar cikakken y@ƙi da Ir@n, kuma wasu na ganin hakan na iya faruwa a ƙarshen wannan makon. A halin da ake ciki kuma, ana zargin wasu na kusa da Tr0mp suna sayen…
Ay Abdullahi1 min read

Da Dumi-Duminsa:Iran Na Shirin Bayyana Wani Sabon Makami Mai Hatsarin Gaske Da Ta Lakaba Wa Suna “Uban Dukkan Bama-bamai”
Da Dumi-Duminsa:Iran Na Shirin Bayyana Wani Sabon Makami Mai Hatsarin Gaske Da Ta Lakaba Wa Suna “Uban Dukkan Bama-bamai”Kakakin rundunar juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC), Hossein Mohebi, ya…
Ay Abdullahi1 min read

Wace ƙasa ce Azerbaijan, ƙasar da ke iyaka da Iran kuma mafi rinjayen al'ummarta ƴan Shi'a, amma suke da kyakkyawar alaƙar difilomasiyya da Isra'ila, amma Iran bata taɓa kai mata farmaki ba?
Wace ƙasa ce Azerbaijan, ƙasar da ke iyaka da Iran kuma mafi rinjayen al'ummarta ƴan Shi'a, amma suke da kyakkyawar alaƙar difilomasiyya da Isra'ila, amma Iran bata taɓa kai mata farmaki ba?Ga…
Ay Abdullahi2 min read