Skip to content
TimesPosts homeTimesPostsThe record, as it happens.

Jinin Al’ada Na Iya Zama Wani Abu Mai Muhimmanci Ga Magunguna Anan Gaba

Jinin Al’ada Na Iya Zama Wani Abu Mai Muhimmanci Ga Magunguna Anan Gaba.Abin da mata da yawa suke zubarwa duk wata, masana kimiyya sun gano cewa yana ɗauke da wasu ƙwayoyin da za su iya taimakawa…

Ay Abdullahi · Admin

· 1 min read

Jinin Al’ada Na Iya Zama Wani Abu Mai Muhimmanci Ga Magunguna Anan Gaba.

Abin da mata da yawa suke zubarwa duk wata, masana kimiyya sun gano cewa yana ɗauke da wasu ƙwayoyin da za su iya taimakawa wajen gyaran jiki.

A cikin jinin al’ada akwai wasu ƙwayoyin da ake kira menstrual blood-derived stem/stromal cells. Masu bincike sun gano cewa suna iya yawaita cikin sauri saboda suna da wasu halaye da ya sa masana kimiyya bincikarsu domin amfani a regenerative medicine, wato magungunan da ke taimakawa jiki wajen gyara lalacewar naman jiki ko za su iya taimaka wa jiki wajen gyarawa ƙwayoyin da suka lalace.

Abin da ya fi ban sha’awa shi ne, wasu gwaje-gwajen akan dabbobi sun nuna cewa waɗannan ƙwayoyin na iya taimakawa wajen saurin warkar da raunuka da sake gina naman jiki.

A wani sabon bincike da aka yi a 2026, masana sun gwada waɗannan ƙwayoyin a kan berayen da suka samu ciwon zuciya. Abin mamaki, ƙwayoyin da aka samo daga jinin al’ada sun taimaka wajen inganta aikin zuciyar berayen, sannan suka rage wasu alamomin lalacewar huhu.

Wannan ba yana nufin an riga an tabbatar da cewa jinin al’ada magani ne akan mutane ba. Wannan bincike har yanzu yana cikin matakin gwaje-gwajen laboratory akan dabbobi kafin mutane.

Zaku iya amfani da jinin al'ada a matsayin maganin gyara da lafiyar jiki?

Sources: PubMed/NIH; Journal of Translational Medicine; Regenerative Therapy (2026).

#DigitalPsychologist @topfans

More from TimesPosts

Jinin Al’ada Na Iya Zama Wani Abu Mai Muhimmanci Ga Magunguna Anan Gaba | TimesPosts